Amurka da Kanta Ta Yi Ta’aziyya bayan Rasuwar Malamin Musulunci a Najeriya
- Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya yi jimamin rasuwar malamin Musulunci da ya rasu a jihar Plateau bayan fama da jinya
- An tabbatar da rasuwar Imam Abdullahi Abubakar, malamin Musulunci da ya ceci Kiristoci 300 a rikicin Plateau da ya faru a 2018
- Marigayi Imam Abdullahi ya shahara a duniya saboda jajircewarsa wajen kare rayuka ba tare da la’akari da addini ba a hare-haren 2018
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bayyana alhininsa game da rasuwar malamin Musulunci, Imam Abdullahi Abubakar a jihar Plateau.
An sanar da rasuwar malamin Musulunci da ya shahara wajen kare Kiristoci a rikicin jihar Plateau a ranar Juma'a 16 ga watan Janairun 2026.

Source: Facebook
Legit Hausa ta samu sakon ta'aziyyar Amurka ne a yau Laraba 21 ga watan Janairun 2026 a shafin U.S. Mission Nigeria da aka wallafa a X.
Abin da ya daukaka Imam Abdullahi Abubakar
Marigayi Imam Abdullahi, wanda ya kasance babban limamin kauyen Nghar da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Plateau, ya rasu yana da shekaru 92 a duniya.
Imam Abdullahi ya samu karɓuwa a cikin gida da waje bayan da ya ɓoye Kiristoci sama da 300 a gidansa yayin hare-haren da suka auku a jihar Plateau a shekarar 2018.
Sakamakon wannan jarumtaka tasa, gwamnatin tarayya ta zaɓe shi domin samun lambar yabo ta ƙasa, 'Member of the Order of the Niger' (MON), inda marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi gaisa da shi
A shekarar 2019, gwamnatin Amurka ta ba shi lambar yabo ta 'International Religious Freedom Award', tana yabawa jajircewarsa da sadaukar da rayuwarsa domin ceto wasu.

Source: Original
Yabon da Amurka ta yi kan Imam Abdullahi
A cikin sanarwar, ofishin jakadancin Amurka ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen dattijo mai juriya da fahimtar juna tsakanin addinai.
Sanarwar ta ce halayensa sun zama abin koyi na zaman tare da juna cikin lumana, tare da jaddada cewa tarihin zaman lafiyarsa zai ci gaba da wanzuwa a zukatan mutane.
A yayin hirarraki bayan lamarin, Imam Abdullahi ya bayyana cewa ceton rayuka wajibi ne a kowane hali, ba tare da la’akari da bambancin addini ba.
Ya ce abin da ya yi ya samo asali ne daga tausayi da girmama bil’adama, yana mai cewa hakan ne ginshiƙin rayuwarsa.
Gwamnan Plateau ya tura sakon ta'aziyya
Shi ma gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi jimamin rasuwar marigayin, inda ya bayyana shi a matsayin mai son zaman lafiya, haɗin kai da shugabanci na sadaukarwa.
Gwamnan ya ce Imam Abdullahi Abdullahi ya bar tarihi mai ɗorewa wanda zai ci gaba da zama abin koyi ga al’ummar Najeriya baki ɗaya, cewar Leadership.
CAN ta tura ta'aziyya bayan rasuwar malamin Musulunci
Mun ba ku labarin cewa Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta yi alhinin rasuwar Malam Abubakar Abdullahi wanda ya rasu yana da shekara 90.
Shugaban CAN, Daniel Okoh, ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya nuna jarumta ta musamman saboda kare rayukan Kiristocin da ya yi.
Kungiyar CAN ta mika ta'aziyya ga iyalan marigayin wanda ta bayyana a matsayin mutumin da ya mutunta ran dan Adam.
Asali: Legit.ng

