Babban Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Habibu Yahaya Kaura Ya Rasu

Babban Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Habibu Yahaya Kaura Ya Rasu

  • Babban malamin Izala, Sheikh Habibu Yahaya Kaura, ya rasu bayan doguwar jinya da ya yi a wani asibiti a birnin tarayya Abuja
  • Malaman Musulunci a Najeriya sun tabbatar da rasuwarsa tare da bayyana alhini da addu’o’i ga marigayin da jajantawa iyalansa
  • Rasuwar malamin ta girgiza al’umma, yayin da ake jiran sanar da lokacin jana’izarsa da karin bayani daga kungiyar Izala ta kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Al’ummar Musulmi a Najeriya sun shiga jimami bayan rasuwar babban malami, Sheikh Habibu Yahaya Kaura, wanda Allah ya karɓi rayuwarsa bayan shafe lokaci yana fama da jinya.

An tabbatar da rasuwar malamin ne a yau Laraba, 21, Janairu, 2026, wanda ya yi daidai da 2, Sha’aban, 1447, a wani asibiti da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci

Sheikh Habibu Yahaya Kaura
Marigayi Sheikh Habibu Yahaya Kaura. Hoto: Zauren Sheikh Habibu Yahaya Kaura
Source: Facebook

Malamin Musulunci, Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna na cikin wadanda suka sanar da rasuwar Sheikh Habibu Yahaya Kaura a shafinsa na Facebook.

Rasuwar Sheikh Habibu Yahaya Kaura ta janyo alhini mai yawa, musamman ganin irin gudunmawar da ya bayar tsawon shekaru wajen wa’azi da karantar da al’umma addinin Musulunci.

Sheikh Habibu Yahaya Kaura ya rasu

Sheikh Kabir Asgar ya sanar da rasuwar malamin ta hanyar wallafa sako a Facebook, inda ya bayyana cewa bayan doguwar jinya Allah Ya yi wa Sheikh Habibu Yahaya Kaura rasuwa.

A cikin sakon, ya jaddada cewa rai baƙon duniya ne, tare da roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin, Ya yi masa rahama, Ya kuma sanya jinyar da ya sha ta zama kaffara gare shi.

Ana jimamin rashin Habibu Yahaya Kaura

Shi ma Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya tabbatar da rasuwar Sheikh Habibu Yahaya Kaura, inda ya bayyana alhininsa tare da kalaman Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.

Kara karanta wannan

Ribadu ya tafka babban rashi, Allah ya karbi ran 'mahaifiyarsa' tana da shekaru 86

Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya bayyana marigayin a matsayin uba kuma masoyi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar addini da al’umma.

Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna
Sheikh Ibrahim Kaduna da ya sanar da rasuwar Sheikh Habibu Yahaya Kaura. Hoto: Ibrahim Aliyu Kaduna
Source: Facebook

Shi ma Sheikh Mansur Ibrahim Sokoto ya wallafa sakon ta'aziyya a shafinsa na Facebook tare da cewa malamin ya bayar da gudumawa wajen yada addini.

Haka zalika Sheikh Jabir Sani Mai Hula ya wallafa a Facebook cewa marigayin yana yawan kiransa ya masa nasiha a kan ikilasi.

Gudunmawar Sheikh Habibu Yahaya Kaura

Sheikh Habibu Yahaya Kaura ya shafe shekaru masu yawa yana wa’azi a sassa daban-daban na Najeriya, inda ya yi fice wajen tafsiri.

An ce ya kasance daya daga cikin fitattun malaman Izala da suka yi tasiri wajen ilmantar da al’umma, musamman matasa, kan fahimtar Musulunci da nisantar bidi’a.

Wasu bayanai sun nuna cewa rasuwar ta faru ne a Asibitin Nizamiyya da ke Abuja, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a fitar da sanarwar lokacin jana’izar marigayin ba.

Duk da haka, jama’a sun fara tura sakonnin ta’aziyya da addu’o’i a kafafen sada zumunta, suna roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya yalwata kabarinsa, Ya kuma sanya Aljanna Firdausi ta zama makomarsa.

Kara karanta wannan

CAN ta yi jimamin rasuwar malamin Musulunci da ya ceci Kiristoci a Rikicin Plateau

Babban Limamin Ilorin ya rasu a Kwara

A wani labarin, mun kawo muku cewa babban limamin Ilorin a jihar Kwara, Sheikh Muhammad Bashir Saliu ya rasu bayan fama da jinya.

Mai Martaba Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari ya tabbatar da rasuwar malamin tare da rokon Allah ya gafarta masa kurakuransa.

Shugabanni, 'yan siyasa, malamai da sauran al'umma a ciki da wajen jihar Kwara na cigaba da addu'o'i ga marigayi Sheikh Saliu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng