Tashin Hankali: Mutum Ɗauke da Adda Ya Tarwatsa Masu Ibada, Ya Ce Ana Damunsa
- Wani bidiyo ya bazu inda aka ga wani mutum dauke da adda ya kutsa cocin yana korafin damunsa da ake yi
- Mutumin ya umurci masu ibada su fita daga cocin yayin da suke kokarin kwantar masa da hankali, hakan ya janyo muhawara a kafafen sada zumunta
- Daga masu tir da shi sai wasu da suka goyi bayan korafinsa kan gurbatar muhalli da hayaniya daga coci a unguwanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - An shiga firgici a jihar Abia bayan wani mutumi dauke da adda ya shiga coci cikin bacin rai saboda yawan damunsa da ake yi
Ra’ayoyi masu zafi sun biyo bayan bidiyon da ya yadu, inda aka ce wani mutum ya shiga coci yana yin barazana ga masu ibada.

Source: Original
A bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta da Punch ta gano, an ga mutumin tsaye a cikin cocin yana umartar masu ibada su fice.

Kara karanta wannan
Mutanen Dorayi sun fadi ainihin abin da ya faru kan kisan Fatima da yaranta 6 a Kano
Yadda kararrakin coci ke damun mutane
Irin wannan kara daga wuraren ibadu da dama ya sa wasu gwamnatoci ke sanya doka domin daidaita sautuka da ke fita daga coci-coci.
A shekarar 2024, gwamnatin Lagos ta kakaba doka da ta tanadi cin tara da hukunci mai tsanani kan wadanda suka saba doka.
Mutumi da makami ya watsa masu ibada
Lamarin ya faru ne a Ibeku da ke birnin Umuahia, jihar Abia inda mutumin dauke da adda ya ce ana damunsa.
An gano wasu daga cikin mambobin cocin har da dattawa na kokarin kwantar masa da hankali da rarrashinsa.
Lamarin ya jawo muhawara a shafukan sada zumunta inda jama’a ke bayyana ra’ayoyi daban-daban kan matsalar hayaniya daga wuraren ibada a unguwanni.
Wani mai amfani da X, @ChuksEricE shi ma ya wallafa bidiyon a shafinsa inda ya ce lamarin bai yi dadi ba ko kada.
A cikin rubutunsa, ya ce:
"Wani mutum ya tayar da tarzoma a wani shirin taron daren addu’a na coci da addaba, sakamakon korafin hayaniya, a Ibeku, Umuahia, Jihar Abia."

Source: Getty Images
Mutane sun bayyana ra'ayoyinsu
Mutane da dama suka ce hayaniya ba daidai ba ce, amma sun soki ‘yan cocin saboda barin mutumin ya shigo dauke da makami ba tare da taka masa birki ba.
Wata mai sharhi ta ce ko da ba hanya ce mai kyau ba, watakila mutumin ya bi hanyoyin doka amma babu wanda ya saurare shi har ya kasa hakuri.
Wasu sun ce cocin na iya fuskantar shari’a saboda rashin sanya ka'ida na sauti, inda suka jaddada cewa hayaniyar coci-coci na Pentecostal na damun mazauna yankuna da dama.
Wani ya yanka ladanin masallaci a Kano
A baya, kun ji cewa al’ummar Hotoro Maraba a Kano sun shiga firgici bayan wani matashi ya kashe ladanin masallaci a lokacin sallar Asubahi.
Rahotanni sun ce rikici ya fara ne bayan ladani ya ce lokacin sallah bai yi ba, lamarin da ya fusata matashin ya yanke makogoronsa.
'Yan sanda sun dauki mataki a yankin domin hana barkewar tarzoma bayan fusatattun matasa sun yi kukan kura sun kashe matashin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
