Albashi: Miliyoyin da Shugaban Ƙasa, Mataimaki da Sauran Jami'an Gwamnati Suke Karba
- Alkaluman hukumar tattara kudin shiga da kasafin kudi (RMAFC) sun bayyana ainihin albashin da Najeriya ke biyan Shugaban Kasa da wasu manyan jami'a
- Rahoton ya nuna cewa adadin albashin da ake biya manyan shugabanni bai yi daidai da yadda jama’a ke tsammani ba, kamar yadda wasu suka bayyana
- Jama'a sun bayyana ra'ayoyi daban-daban a kan wannan batu, amma suna ganin watakila kankantar albashin ya kara yawan rashawa a kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Alkaluman hukumar tattara kudin shiga da kasafin kudi (RMAFC) sun bayyana ainihin albashin da kasar nan ke biyan Shugabannin kasa.
Haka kuma an gano yawan kudin da ake biyan wasu manyan jami'an gwamnati da ma'aikatan da ke bangaren shari'a bisa tanadin doka

Kara karanta wannan
Kisan Fatima: Sheikh Daurawa ya yi magana mai ratsa zuciya kan ta'addancin da aka yi a Kano

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa wadannan alkaluma sun shafi albashin shekara-shekara ne kawai, ba tare da haɗa alawus, kari, ko wasu albarkatun ofis ba.
Albashin Shugaban kasa da jami'an gwamnati
Alkaluman sun bayyana cewa Shugaban ƙasa na Najeriya yana karɓar albashin Naira miliyan 3.51 a shekara, yayin da Babban Alƙalin Alƙalai na Najeriya ke samun Naira miliyan 3.36.
Mataimakin shugaban ƙasa yana da albashin Naira miliyan 3.03 a shekara. Alƙalin Kotun Ƙoli da Shugaban Kotun Daukaka Ƙara suna karɓar naira miliyan 2.48, adadi ɗaya da Shugaban Majalisar Dattawa.
Gwamnan jiha yana samun Naira miliyan 2.22, sai Mataimakinsa Naira miliyan 2.11 a kowace shekara a kasar nan.
Sanata da Minista, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Shugaban Ma’aikata na ƙasa, da shugabannin hukumomin tsarin mulki suna karɓar Naira miliyan 2.03
Karamin Ministan a Najeriya da sauran shugabannin hukumomi da tsarin mulki ya amince da su, suna da albashin Naira miliyan 1.96.

Kara karanta wannan
Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci
Mai bai wa Shugaban ƙasa shawara ta musamman yana karɓar naira miliyan 1.94, yayin da manyan mukamai kamar Darakta-Janar, babban sakatare da shugabannin hukumomi da kamfanonin gwamnati, da kuma Kwamishinan Zaɓe na INEC ke samun Naira miliyan 1.93.
Kakakin Majalisar Dokokin Jiha yana karɓar naira miliyan 1.64, yayin da Shugaban Karamar Hukuma ke samun naira 908,312 a shekara.
Ra’ayin jama’a kan albashin Shugaban kasa
Wadannan alkaluma sun haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ’yan Najeriya, inda wasu ke ganin kudin ya yi kadan idan aka kwatanta da girman ofishin Shugabannin/

Source: Facebook
Wani mai amfani da shafin X, @AzeezOpeQuadri, ya ce:
“Don haka Shugaba Bola Tinubu yana samun kusan N292,500 a wata, duk da cewa alawus-alawus na tafiyarsa kaɗai na iya wuce jimillar wadannan albashin na shekara? Mu ci gaba da ruɗar kanmu.”
Shi ma @orjaiski ya bayyana damuwa inda ya ce:
“Idan wannan gaskiya ne, abin takaici ne ƙwarai. Ba abin mamaki ba ne ganin yadda satar dukiya ta yi yawa.”
Shugaban Kasa ya dawo Najeriya
A baya, mun wallafa cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya koma gida Najeriya bayan kammala rangadin da ya ɗauki tsawon makonni uku a ƙasashen waje inda aka gudanar da taruka.

Kara karanta wannan
Tirkashi: Kotu ta tura tsohon shugaban kasa gidan yari, zai yi zaman shekaru 5 a Korea
Dawowarsa ta zo ne bayan halartar Taron Dorewar Ci Gaba na Abu Dhabi na shekarar 2026 (ADSW 2026), wanda aka gudanar a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a makon da ya gabata.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da dawowar Tinubu a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar 17 ga watan Janairu, 2026 a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng