An kai Hari Dakin Kwanan Dalibai Mata a Jami'ar Gombe, an Raunata Daliba

An kai Hari Dakin Kwanan Dalibai Mata a Jami'ar Gombe, an Raunata Daliba

  • Hukumar Jami’ar Jihar Gombe ta tabbatar da faruwar wani hari da aka kai wa wata daliba a dakin kwanan mata da ke cikin harabar jami’ar da sanyin safiya
  • Dalibar, wadda ke shirin kare karatunta a shekarar karshe, ta samu raunuka yayin da take kokarin kare kanta daga wani bata gari da ya shiga makarantar
  • Hukumar jami’ar ta ce jami’an tsaro sun dauki matakin gaggawa, tare da tabbatar da cewa ana kara tsaurara tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin dalibai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Hukumar Jami’ar Jihar Gombe ta tabbatar da faruwar wani lamari na tsaro da ya shafi kai hari kan wata dalibar shekarar karshe a daya daga cikin dakunan mata.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin, 19 ga Janairun 2026 a lokacin da dalibai ke hutu, kamar yadda jami’ar ta bayyana a wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Bayan kisan Kano, miji ya kashe matarsa da fartanya a Kebbi

Jami'ar jihar Gombe
Kofar shiga jami'ar jihar Gombe. Hoto: Gombe State University, Gombe.
Source: Facebook

Mai magana da yawun jami’ar, Hadu Ligari, ne ya fitar da sanarwar a Facebook, inda ya tabbatar da cewa an riga an dauki matakan gaggawa domin shawo kan lamarin.

Yadda aka kai farmaki jami'ar Gombe

A cewar sanarwar jami’ar, dalibar tana cikin shirin kammala bincike da dalibai ke yi a lokacin gama karatu ne wani bata gari ya shiga wajen kwanan mata tare da kai mata hari.

An bayyana cewa harin ya faru ne da sanyin safiya, lamarin da ya jefa sauran dalibai cikin fargaba kafin jami’an tsaro su kai dauki.

Hukumar jami’ar ta ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’an tsaro sun isa wurin cikin gaggawa domin dakile duk wata barazana da ka iya biyo baya.

Matakin da jami'ar Gombe ta dauka

Jaridar Punch ta wallafa cewa Ligari ya ce jami’an tsaron jami’ar sun dauki mataki cikin hanzari bayan sanar da su abin da ya faru.

Kara karanta wannan

An gano gargadin da aka yi wa Donald Trump har Amurka ta fasa kai hari Iran

Ya bayyana cewa an killace yankin da lamarin ya faru, tare da tabbatar da cewa sauran daliban da ke masaukin suna cikin tsaro.

Hakan ya ba jami’ar damar hana yaduwar tashin hankali da kuma kare lafiyar dalibai da ma’aikata a harabar jami’ar a halin yanzu.

Halin da dalibar ke ciki a yanzu

Sanarwar ta bayyana cewa dalibar ta samu mummunan rauni a hannayenta yayin da take kokarin kare kanta daga harin da aka kai mata.

Sai dai duk da haka, jami’ar ta ce an kai ta asibiti cikin gaggawa, inda aka ba ta kulawar likitoci, kuma ta fara samun sauki a yanzu.

Hukumar ta jaddada cewa ana ci gaba da kula da lafiyar dalibar tare da sanya ido kan yanayinta domin tabbatar da murmurewarta gaba daya.

Bayan faruwar lamarin, shugaban Jami’ar, Farfesa Sani Ahmed Yauta tare da wasu manyan jami’an gudanarwa sun kai ziyara wurin da abin ya faru.

Farfesa Sani Ahmed Yauta
Shugaban jami'ar Gombe, Farfesa Sani Ahmed Yauta. Hoto: Sani Ahmed Yauta
Source: Facebook

An kashe matashi a jihar Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa wani yaron shago a jihar Gombe ya kashe mai gidansa saboda wani sabani da suka samu da ya kai ga korarsa.

Kara karanta wannan

Soja ya samu rauni da gobara ta kama gidan sojoji, ta kona masallacinsu a Yobe

Matashin mai suna Abdulaziz Ibrahim Aliyu ya rasu ne bayan yaron shagon ya caka masa almakashi saboda ya umarce shi ya bar masa shago.

Wani rahoto ya nuna cewa yaron shagon ya kashe Abdulaziz ne a gaban mahaifiyarsa, lamarin da ya kara jan hankulan al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng