Kyakkyawar budurwa ta ciri Tuta a jami'ar jihar Gombe, ta karya tarihi
- Wata 'yar Najeriya ta zama abin alfahari ga iyayenta bayan karya tarihi a jami'arta
- Halima ta samu lambobin yabo guda tara duk a lokaci guda
- Mutane da dama sun tofa albarkatun bakinsu kan nasarar da budurwar ta samu
Wata 'yar Najeriya, Halima Yayajo, ta samu gagarumin nasara a jami'ar jihar Gombe, inda ta zama zakarar shekara a fannin ilmin Likitanci.
Wata mai suna Fadilat Idris, ta bayyana hakan a shafinta na Facebook inda ta daura hotunan lambobin yabon da Halima ta samu da kuma hoton bikin yayesu.
KU KARANTA: Za'a fita duba watan Zhul-Hajji ranar Juma'a a kasar Saudiyya
Ta lashe komai
Halima ta samu lambobin yabo guda tara a fannoni daban-daban na karatun koyon Likitanci.
Ta zama zakara a fannin medical biochemistry, histopathology, community medicine, clinical pharmacology, obstetrics & gynecology, ENT, da anaesthesia.
Hakazalika aka alanta ta a matsayin dalibar Likitanci da tayi zarra cikin dukkan sauran daliban tsangayar Likitanci.
DUBA NAN: Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi ba - Bala Mohammed
Yar Buhari ma ta yi digirgir
Hanan ‘yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta samu digiri na biyu a fannin daukar hoto.
Bayo Omoboriowo, mai daukar hoto na musamman ga shugaba Buhari ne ya sanar da hakan a wani hoton bidiyo inda yake taya ta murna.
Ba a bayyana ko wace jami'a ce ta kammala digirin ba amma faifan bidiyon ya nuna tana tafe kan dandamali tare da wasu fararen malamanta da ke ba ta lambar yabo.
Asali: Legit.ng