An Yi Kira a Fara Shirin Ramadan, Sarkin Musulmi Ya Sanar da Shigowar Sha'aban 1447

An Yi Kira a Fara Shirin Ramadan, Sarkin Musulmi Ya Sanar da Shigowar Sha'aban 1447

  • Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya sanar da cewa Talata, 20, Janairu, 2026 ita ce ranar farko ta watan Sha’aban 1447AH
  • An yanke wannan hukunci ne bayan kammala duban jinjirin watan Sha’aban a fadin Najeriya, inda aka tabbatar da ganin watan a hukumance
  • Sha’aban na zuwa ne gabanin watan hijira na tara, lamarin da ke nuni da cewa saura wata guda kacal a fara azumin Ramadan na shekarar 1447Ah

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana Talata, 20, Janairu, 2026 a matsayin ranar farko ta watan Sha’aban 1447.

Sanarwar ta fito ne daga Majalisar Masarautar Sokoto a daren Litinin, 19, Janairu, 2026, bayan kammala aikin duba jinjirin wata a sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano babban rumbun ajiyar kayan Boko Haram a karkashin kasa

Mai alfarma Sarkin Musulmi da wata a gefensa.
Mai alfarma Sarkin Musulmi a hagu, wata a gefen dama. Hoto: HQ Nigerian Army|Getty Images
Source: Facebook

Sanarwar da Kwamitin ganin wata wato MNSC ta fitar a X ta samu sa hannun Wazirin Sokoto kuma Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini, Farfesa Sambo Wali Junaidu.

Ana hararo Ramadan bayan shigowar Sha'aban

A cewar sanarwar, ayyana ranar Talata 20 ga Janairun 2026 a matsayin farkon Sha’aban ya biyo bayan tabbacin ganin jinjirin wata a duba watan da aka gudanar a matakin kasa.

Kwamitin ya bayyana cewa wannan mataki ya yi daidai da koyarwar Musulunci da kuma tsarin duban wata da ake bi a Najeriya karkashin jagorancin Sarkin Musulmi.

Hakan ya tabbatar da kammala watan Rajab tare da shiga sabon wata na Sha’aban, wanda ke da muhimmanci sosai a kalandar Musulunci.

Muhimmancin watan Sha’aban a Musulunci

Kara karanta wannan

Kalaman da aka ji Tinubu ya fada bayan tabbatar da Rasuwar Sheikh Muhammad Bashir Saliu

Rahotanni sun nuna cewa Sha’aban wata ne na takwas a kalandar Musulunci kuma shi ne watan da ke gab da Ramadan, watan azumi mafi falala ga Musulmi.

Wani malamin Musulunci, Sheikh Usman Al-Juzuri ya ce ana so Musulmi da su yi shiri mai kyau domin tunkarar azumin Ramadan a Sha'aban.

Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri
Sheikh Usman Al-Juzuri yana gabatar da karatu. Hoto: Naziru Usman
Source: Facebook

A cewarsa, da zarar an shiga Sha’aban, an shiga kirga kwanaki zuwa watan Ramadan, inda ake sa ran fara azumi bayan cikar wata guda.

Kasancewar Ramadan wata ne da Musulmi ke azumi daga wayewar gari zuwa faduwar rana, tare da yawaita salla, karatun Alkur’ani, sadaka da kuma kyautata dabi’u, malamin ya ce:

"Wannan lokaci na Sha’aban na bai wa al’umma damar gyara alaka da Allah da kuma juna, domin samun Ramadan mai albarka da natsuwa."

Umarnin duba jinjirin watan Sha'aban 1447

A wani labarin, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bayar da umarnin duba watan Sha'aban 1447.

A sanarwar da ya fitar, ya umarci dukkan al'ummar Musulmi su fita su duba watan sannan su sanar da hakimai mafi kusa da su idan sun ga jinjirin wata.

Fadar Sarkin Musulmi ta sanar da cewa za a tantance dukkan bayanan da wadanda suka sanar da cewa sun ga wata kafin a sanar da 'yan kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng