Sojoji Sun Gano Babban Rumbun Ajiyar Kayan Boko Haram a karkashin Kasa
- Sojojin Operation Hadin Kai sun lalata sansanonin Boko Haram a yankin Timbuktu Triangle tare da gano rumbun ajiya a karkashin kasa
- Rahotanni sun nuna cewa an samu man fetur, kayan magani da makamai yayin farmakin da aka kai a wurare daban-daban na Jihar Borno
- Duk da hare-haren jiragen sama marasa matuka daga ’yan ta’adda, sojoji sun ci gaba da farmaki tare da korar su a yankin Arewa maso Gabas
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno – Rundunar sojin Najeriya da ke karkashin Operation Hadin Kai ta samu gagarumar nasara bayan gano wani rumbun ajiyar kayan aiki na Boko Haram da ke karkashin kasa a Jihar Borno.
Wannan nasara ta zo ne bayan jerin hare-haren da aka shirya bisa sahihan bayanan sirri a yankin Timbuktu Triangle, inda sojoji suka mamaye sansanonin ’yan ta’adda da dama.

Kara karanta wannan
Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan bama bamai a Borno, mutane fiye da 40 sun mutu

Source: Facebook
A sakon da rundunar ta wallafa a X, ta ce farmakin ya taimaka wajen raunana karfin aiki da dabarun Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas.
Yadda sojoji suka farmaki Boko Haram
A ranar 18, Janairu, 2026, sojojin Operation Hadin Kai sun bar sansanoninsu suka kaddamar da hare-hare a yankunan Chilaria, Garin Faruk da Abirma. Wadannan hare-hare sun kasance bisa tsari da bayanan sirri da aka tattara tun da fari.
A yayin ci gaban farmakin, an tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda tare da tilasta musu tserewa daga maboyarsu. Rundunar ta ce wannan mataki ya taimaka wajen karya tsarin tafiye-tafiye da hanyoyin sadarwar Boko Haram a yankin.
Sojojin sama sun taka muhimmiyar rawa ta hanyar sanya ido da bayar da bayanai kai tsaye, abin da ya bai wa dakarun kasa damar gano inda ’yan ta’adda suke.
An gano rumbun ajiyar Boko Haram
A yayin aikin share yankin, sojoji sun gano kayayyaki da makamai da dama da suka hada da rediyon Baofeng, wayoyi, alburusai na AK-47 da harsasan bindiga na musamman.
Haka kuma an gano tutocin Boko Haram da ISWAP, injinan niƙa masu amfani da dizal, manyan buhunan hatsi da wata mota kirar a kori kura.
Mafi daukar hankali shi ne gano rumbun ajiyar kayan aiki a karkashin kasa, inda aka adana man fetur, man shafawa da kuma magani, lamarin da ke nuna yadda ’yan ta’addan ke shirya kansu a daji.
Punch ta rahoto cewa rundunar ta ce yanayin tsaro a yankin ya lafa amma har yanzu akwai barazanar kai hare-haren ba zata. Saboda haka, sojoji na ci gaba da kasancewa cikin shiri.

Source: Facebook
An yi gargadi kan sakin 'yan ta'adda
A wani rahoton, kun ji cewa dattawan jihar Katsina sun fara martani kan shirin gwamnatin jihar na sakin 'yan bindiga 70 domin sulhu.
Daya daga cikin dattawan jihar, Dr Bashir Kurfi ya bayyana cewa ba su goyon bayan shirin kuma za su ga wanda zai amince da shi a jihar.
A bayanin da ya yi, Dr Kurfi ya ce 'yan bindiga masu fashi da garkuwa da mutane sun fi Boko Haram hadari, saboda haka babu dalilin sakinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
