Kisan Fatima da Yaranta: Daurawa Ya Jero Matakan da za a Bi don Hukunta Su Umar

Kisan Fatima da Yaranta: Daurawa Ya Jero Matakan da za a Bi don Hukunta Su Umar

Shugaban hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da yi wa Fatima Abubakar da yaranta adalci.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa hanyoyi da matakai da suka dace a bi wajen tabbatar da adalci kan kisan Fatima Abubakar da yaranta.

Sheikh Daurawa ya fadi matakan hukunta su Umar
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da yaran Fatima da aka kashe a Kano Hoto: Imam Dr. Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

A cikin wani bidiyo da Musbahu Muhd Fada ya wallafa a Facebook, Daurawa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Haruna, mijin Fatima Abubakar, wadda aka kashe tare da yaranta gaba ɗaya.

Ya ce hanyoyin da za a bi sun haɗa da:

1. Binciken ’yan sanda

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa mataki na farko wajen tabbatar wa Fatima da dukkan yaranta adalci yana hannun ’yan sanda.

Kara karanta wannan

Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci

A kalaman fitaccen malamin:

“Na farko shi ne na ’yan sanda, ’yan sanda suna nan suna ƙoƙarinsu wajen damƙe, binciko, bankado tare da gano dukkanin waɗanda suke da hannu a cikin wannan ta’addanci.”
“Muna roƙon Allah Ya ba wannan hukuma ta jami’an tsaro nasara, su ci nasara a kan kama duk wanda ya ke da hannu a cikin wannan ta'addanci."

2. Kotu

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya kara da cewa bayan jami'an tsaro sun kammala bincike, za su mika wadanda ake zargi da aikata wannan mummunan kisa ga kotu.

Malamin ya nuna akwai yiwuwar a samu wasu mutane su tsaya wa wadanda akar zargi, su yi kokarin kare su a kotu ta yadda za a gaza yanke masu hukuncin kisa.

Sheikh Daurawa ya ce:

"Idan sun gama bincike kuma alkalai suke tura wa. Ka ga abu ya koma hannun alkalai. Yanzun nan za ka ga wasu kungiyoyi a duniya, marasa imani sun turo sun ce a kare su. Saboda haka aikin alkalai da lauyoyin Musulunci, su tsaya su tabbatar da cewa an yi shari'a."

Kara karanta wannan

Ma'aikatar shari'a: Abin da za mu yi game da kashe Fatima da yaranta 6 a Kano

"Idan alkali ya tabbatar ya samu wadannan da laifi kuma ya yanke masu hukuncin kisa, ya rage saura gwamna."

3. Gwamnan jihar Kano

Shugaban hukumar Hisbah ya kara da cewa da zarar alkalai sun yanke hukuncin kisa a kan wadanda suka aikata wannan kisan gilla, kallo ya koma ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Sheikh Daurawa ya roki gwamna ya tabbata an aiwatar da hukunci a kan wadanda suka kashe Fatima
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A cewarsa:

"Don haka Gwamna, In Sha Allahu, za mu karfafa masa gwiwa, mun san kasashen Turai suna yin ca su ce kada su sa hannu a kan a yi kisa. Amma za mu karfafa masa gwiwa, kuma jajirtacce ne, In Sha Allahu za mu tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan ta'addanci, babu wanda ya kubuta, babu wandaya tsira, babu wanda aka kyale."
"Saboda haka iyalai, lokacin da aka ce an fara wannan shari'a, mu sa ido, lokacin da aka ce an zartar da shari'a mu sa ido."

Sheikh Daurawa ya kara da cewa da zarar an yanke hukuncin kisa, za a dunguma gidan gwamnatin Kano domin a karfafa wa gwamna gwiwa don ya sanya hanya a aiwatar da hukuncin.

Kara karanta wannan

An yanke wa wani dan Najeriya hukuncin kisa, za a rataye shi har lahira

Ya bayyana cewa akwai bukatar jama'a su taimaka wajen sanya idanu a kan al'amuran da ke gudana a unguwanninsu, tare da mallakar makamai domin kare kai ta hanyar da gwamnati ta tanada.

Mahaifin Umar na so a hukunta dansa

A wani labarin, kun ji cewa Malam Auwal, mahaifin Umar da ake zargi da jagorantar kisan wata baiwar Allah mai suna Fatima Abubakar tare da dukkannin yaranta a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano ya yi magana.

Malam Auwal ya bayyana takaici da kuncin da ya shiga bayan an samu hujjojin da ke bayyana cewa 'dansa na da hannu a kisan 'yar uwarsa da yaranta har cikin gida, kuma ya barranta kansa da Umar da ya yi wannan aiki.

Umar, tare da wasu mutane biyu, na hannun jami’an ’yan sandan jihar Kano bayan sun amsa laifin shiga gidan Fatima Abubakar tare da kashe ta da yaranta bakwai a ranar Asabar, 17 ga watan Janairu, 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng