Shugaba Tinubu Ya Bada Umarni game da Kisan Matar Aure da Yaranta 7 a Kano
- Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa Fatima Abubakar da yaranta shida a unguwar Chiranci dake Kano
- Shugaban kasar ya ba da 'yan sanda sabon umarni yayin da aka ce an kama mutane uku da ake zargi da aikata wannan danyen aikin
- Shugaba Tinubu ya kuma jajanta wa al'ummar jihar Kano bisa rasuwar babban dan kasuwa Alhaji Bature Abdulaziz a karshen mako
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna tsananin damuwarsa tare da yin Allah-wadai da kisan gilla da aka yi wa Fatima Abubakar da yaranta shida.
Wannan danyen aiki ya faru ne a unguwar Chiranci dake cikin birnin Kano, inda mahara suka shiga cikin gidan Fatima, suka kashe ta da dukkan 'ya'yanta.w

Source: Twitter
Umarnin Tinubu kan kisan matar aure
A wata sanarwa da Bayo Onanuga, ya fitar, kuma Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Tinubu ya bayyana kisan a matsayin wani aiki na rashin imani.
Shugaban kasar ya jinjina wa rundunar yan sanda bisa yadda suka yi gaggawar kamo mutane uku da ake zargi da aikata wannan danyen aiki.
Tinubu ya bayyana cewa:
"Ina jinjina wa yan sanda kan kamo manyan wadanda ake zargi, kuma na bada umarnin a gudanar da sahihin bincike akansu."
Ya ci gaba da cewa:
"Dole ne a tabbatar da cewa an gurfanar da wadannan mutane gaban kotu domin su fuskanci hukuncin da ya dace da laifinsu."
Bayanan rundunar yan sandan jihar Kano
Kafin jawabin shugaban kasar, rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta sanar da kama wadanda ake zargin tsakanin daren 17 da asubar 18 ga Janairu, 2025.
CSP Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda aka kama, wanda dan uwan marigayiyar ne, ya amsa laifin kulla wannan kisan gilla.
Legit Hausa ta rahoto mai magana da yawun 'yan sanda ya ce:
"Babban wanda ake zargin ya amsa laifin, sannan ya tabbatar da cewa kungiyarsu ce ke kai hare-hare a sassan birnin Kano daban-daban."

Source: Facebook
Ta'aziyyar rasuwar babban dan kasuwar Kano
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya bayyana alhini kan rasuwar fitaccen dan kasuwar nan na Kano, Alhaji Bature Abdulaziz, wanda ya rasu a karshen makon nan.
Shugaban kasar ya bayyana rasuwar tasa a matsayin babban rashi ga daukacin harkar kasuwanci a Najeriya, ba wai ga jihar Kano kadai ba baki daya.
Sanarwar Onanuga ta rahoto Tinubu yana cewa:
"Marigayi Bature Abdulaziz ya kasance jajirtaccen shugaba wanda ya ba mu gagarumin goyon baya a lokacin yakin neman zabenmu na shekarar 2023."
An ce marigayi Dr. Bature Abdulaziz shi ne shugaban kungiyar hadakar yan kasuwa ta Najeriya, sannan kuma ya kafa kungiyar dattijai masu kishin kasa domin zaman lafiya.
Kano: Mijin Fatima na bukatar taimako
A wani labari, mun ruwaito cewa, al’umma sun fara kira da a hada kai domin taimakawa Malam Bashir Haruna, da aka kashe 'ya'yansa shida da matarsa a Kano.
Barista Abba Hikima ya bayyana jerin abubuwan da ya ce ya kamata a masa da nufin saukaka radadin da mutumin ke ciki tare da farfado da rayuwarsa.
Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnati, attajirai da ’yan jarida su nuna tausayi a mu’amalarsu da wanda abin ya shafa lura da halin da yake ciki.
Asali: Legit.ng


