Mahaifin Umar Ya Barranta da 'Dansa da ake Zargi da Kashe Yar Uwarsa da Yara 7

Mahaifin Umar Ya Barranta da 'Dansa da ake Zargi da Kashe Yar Uwarsa da Yara 7

  • Mahaifin Umar, Malam Auwal, ya barranta kansa da kisan Fatima Abubakar da yaranta a Kano da ake zargin 'dan cikinsa ya aikata
  • Wadanda ake zargi sun shiga hannun ’yan sanda bayan amsa laifin aikata kisan, kuma Umar Auwal ne ake zargin jagoran kisan
  • Kiran mahaifin Umar da aka tabbatar dan uawn Fatima ne ya zo a lokacin da gaba daya mutanen Kano da Arewa suka shiga tashin hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Malam Auwal, mahaifin Umar da ake zargi da jagorantar kisan wata baiwar Allah mai suna Fatima Abubakar tare da dukkannin yaranta a unguwar Dorayi Chiranchi da ke Kano.

Umar, tare da wasu mutane uku, na hannun jami’an ’yan sandan jihar Kano bayan sun amsa laifin shiga gidan Fatima Abubakar tare da kashe ta da yaranta bakwai a ranar Asabar, 17 ga watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar shari'a: Abin da za mu yi game da kashe Fatima da yaranta 6 a Kano

Mahaifin Umar ya nemi a hukunta dansa
Umar da ake zargi da kashe mutum 7 a Kano, Fatima da yaranta Hoto: Hussaina Abkr
Source: Facebook

A cikin wani labari da Freedom Radio ta wallafa a shafin Facebook, mahaifin Umar ya tabbatar da cewa babu shi, babu Umar da ya amsa aikata wannan danyen aiki.

Mahaifin Umar ya shiga kunci kan kisan Fatima

Malam Auwal ya bayyana cewa ya barranta kansa gaba ɗaya da abin da ake zargin dansa ya aikata, inda ya bayyana cewa akwai bukatar a zartar da hukunci.

Ya roƙi mahukunta da su gaggauta yanke hukunci a kan wannan danyen aiki da aka aikata, domin ya zama izina ga wasu da ka iya tunanin aikata irin wannan laifi a nan gaba.

Ya jaddada cewa adalci shi ne kadai abin da ake bukata a halin da aka kashe na samun mummunan labarin abin da dansa da wasu mutum 2 suka aikata.

Za a hukunta matasan da suka kashe Fatima

Ba mahaifin Umar ne kawai ke son a tabbatar da adalci ba, ita ma Ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta bayyana fatan cewa bangaren zartarwa zai yi duk abin da ya dace wajen tabbatar da an zartar da duk wani hukunci da kotu za ta yanke.

Kara karanta wannan

Bayan kisan Kano, miji ya kashe matarsa da fartanya a Kebbi

Ana fatan za a zartar da hukunci a kan Umar da abokansa biyu
Mijin Fatima da yaransa 6 da aka kashe a Kano Hoto: Kwankwasiyya Trustworthy NG
Source: Facebook

Kakakin Ma’aikatar shari’a ta Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya jaddada cewa daga bangarensu ba za a yi wasa, jinkiri ko jan kafa ba a wannan shari’a.

Ya bayyana cewa ma’aikatar ta kuduri aniyar bin shari’ar tun daga farko har zuwa karshe domin ganin doka ta yi aiki.

Sai dai Baba Jibo ya yi nuni da cewa duk da kokarin da kotuna ke yi wajen yanke hukunci bisa tanadin doka, akwai bukatar bangaren zartarwa ma ya shirya tsaf domin aiwatar da hukuncin da za a yanke nan gaba.

An kama makasan Fatima da yaranta

A baya, mun wallafa cewa rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, bisa umarnin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a kisan gilla a Kano.

Kakakin rundunar a Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi 18 ga watan Janairu 2026, kwanda daya da mummunan lamarin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mutum 3 da ake zargi da kashe matar aure da yaranta 6 a Kano

Ya ce rundunar ba ta yi kasa a gwiwa ba tun bayan faruwar lamarin, inda jami’ai suka fara tattara bayanai, bin diddigin alamu da hada kai da wasu sassan tsaro domin tabbatar da an kama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng