Dattawan Katsina Sun Shiga Maganar Sakin 'Yan Bindiga 70, Sun Zafafa Kalamai
- Jagoran rundunar Katsina Community Security Initiative, Dr Bashir Kurfi, ya yi kakkausar suka kan shirin sakin wasu ’yan fashin-daji da aka kama
- Rahotanni sun nuna cewa Kurfi ya ce sulhun da ake yi da ’yan fashin-daji a Katsina yana kara musu karfi tare da jefa jihohi cikin sabuwar matsala
- Malamin ya jaddada cewa sakin ’yan ta’adda bayan kama su, kuma kotu ta yi mx ceu hukunci yana raunana doka da oda, tare da bata kokarin jami’an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina — Jagoran Katsina Community Security Initiative, Dr Bashir Kurfi, ya bayyana rashin amincewarsa da duk wani yunkuri na sakin ’yan fashin-daji da aka kama a jihar Katsina, yana mai cewa hakan barazana ce ga tsaron al’umma.
Dr Kurfi ya ce a bayyane yake cewa sakin ’yan ta’adda, musamman wadanda aka kama da laifuffukan fyade da kisan kai, ba zai kawo zaman lafiya ba.

Source: Facebook
A bidiyon da BBC Hausa ta wallafa a X, ya ce wannan mataki yana kara wa ’yan bindiga karfin guiwa tare da jefa al’ummar cikin matsi a Katsina
Dr Bashir Kurfi ya ce babban kuskure ne a ce jami’an tsaro sun kama barayi, kotu ta gurfanar da su ta kuma yanke musu hukunci, daga bisani kuma a zo a ce a sake su saboda wasu ’yan siyasa sun shiga maganar.
A cewarsa, sulhun da aka yi a baya ya bai wa ’yan bindiga damar sake shirya kansu. Ya ce bayan an ce an yi sulhu, wasu daga cikin barayin sun fito fili suna sayen makamai da kayan aiki ba tare da tsoro ba.
Har ma, a cewarsa, suna shiga gidajen mai su saye fetur kowa na kallonsu, suna fakewa da hujjar cewa hukumomi sun yi sulhu da su.
Bambancin Boko Haram da 'yan bindiga
A wani bangare na kalamansa, Kurfi ya ce ko Boko Haram akwai wadanda ke ba su umarni da tsari, amma ’yan fashin-daji kowa gashin kansa ya ke ci.
A karkashin haka ya ce gwara 'yan Boko Haram a kan 'yan bindiga duk da cewa dukkansu 'yan ta'adda ne da ake Allah wadai da su.
Ya ce yawancin ’yan fashin-dajin ’yan asalin Katsina ne, kuma an san iyayensu da danginsu. Ya bayyana cewa an taba tattaunawa da wasu daga cikin iyayensu.
Dr Bashir Kurfi ya ce akwai bukatar a samu matsaya daya tsakanin gwamnatin jihar Katsina da ministan tsaro. Ya nuna damuwa kan yadda ministan tsaro ke cewa babu sulhu, yayin da a gefe guda gwamnati ke ci gaba da kokarin yin sulhu.
Kurfi ya ce har yanzu yana jiran ganin wani dattijo ko alkali da zai fito fili ya ce a saki ’yan bindiga 70 da aka kama abu ne da ya dace.

Source: Facebook
Barazanar Turji ta firgita 'yan Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan ta'adda, Bello Turji na cigaba da yi wa jama'a barazana a jihar Sokoto da wasu sassan Arewacin Najeriya.
Saboda barazanar kai hari da dan ta'addan ya yi a Sokoto, mutane da dama sun fara kaura daga jihohinsu zuwa Jamhuriyar Nijar domin neman tsira.
Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan Najeriya da suka fake a Nijar na cikin mawuyacin hali lura da yadda ba su samun abinci ko wajen kwana.
Asali: Legit.ng

