Abba, Barau da Hukumomi 2 da Suka Yi Alkawarin Nema wa Fatima da Yaranta 6 Adalci

Abba, Barau da Hukumomi 2 da Suka Yi Alkawarin Nema wa Fatima da Yaranta 6 Adalci

Tun bayan bullar mummunan labarin kisan gilla da aka yi a Jihar Kano a ranar Asabar, 17 ga watan Janairu, 2026, yankin Arewa baki ɗaya ya shiga cikin jimami da alhini mai tsanani.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoKisan wata mata mai suna Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi, ya girgiza zukatan ’yan Najeriya tare da jawo martani daga manyan jami’an gwamnati da hukumomin tsaro.

Gwamna, Sanata Barau da hukumomi sun yi alkawarin tabbatar da adalci kan kisan bayin Allah a Kano
Umar da ake zargin ya ja tawaga an kashe mutum 7 a Kano, Fatima da yaranta Hoto: Hussaina Abkr
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan wasu muhimman mutane da hukumomi da zuwa yanzu suka yi alkawarin tabbatar da ganin an yi adalci kan wannan mummunan aika-aika da ake zargin Umar Auwalu tare da wasu mutum uku sun aikata.

Daga cikin wadanda suka yi alkawari a kan wannan al'amari sun hada da:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta shige gaba don shari'a kan kisan matar aure da yaranta 6

1. Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, shi ma ya bayyana matuƙar baƙin ciki kan kisan Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida.

BBC Hausa ta wallafa cewa gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai yi binciken tare da jagorantar shari'a da matasan da suka amsa cewa sun yi kisan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin imani, marar dalili, kuma cin mutunci ga darajar rayuwar dan Adam.

Gwamnan Kano ya yi alkawarin tabbatar wa Fatima da yaranta adalci
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sanarwar da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu, ta nuna cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da abin ya shafa, mazauna Dorayi Chiranchi da daukacin al’ummar Jihar Kano.

Ya kuma roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa mamatan tare da ba iyalansu haƙurin jure wannan rashi.

Gwamna Abba ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci aikata laifuffuka masu tayar da hankali ba, yana mai cewa za a bi dukkannin hanyoyin doka domin ganin an hukunta mutanen.

Kara karanta wannan

Mahaifin Umar ya barranta da 'dansa da ake zargi da kashe yar uwarsa da yara 7

2. Barau Jibrin

Jaridar eadership ta wallafa cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yaba wa rundunar ’yan sandan jihar Kano kan gaggawar kama mutane uku da ake zargi da kisan Fatima da yaranta.

Sanatan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Malam Ismail Mudashshir, ya fitar a ranar Lahadi, 19 ga watan Janairu, 2026.

Sanata Barau ya yi alkawarin bibiyar batun kisan mutum bakwai don a samu adalci a Kano
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Sanata Barau Jibrin ya ce kama wadanda ake zargi abu ne da ya kawo wa zuciya sauki, amma ya jaddada bukatar gudanar da bincike mai zurfi da kuma hanzarta shari’a domin ganin an hukunta masu laifin.

A cewarsa:

“Na shiga cikin tashin hankali da alhini matuƙa sakamakon kisan wannan uwa da ’ya’yanta marasa laifi. Wannan aiki ne na rashin imani kuma ya wuce tunanin dan Adam.”

3. Yan sandan Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano da ta tabbatar da kama mutane uku da ake zargi da kashe matar aure da yaranta ta sha alwashin an bi masu hakkinsu.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar shari'a: Abin da za mu yi game da kashe Fatima da yaranta 6 a Kano

A sanarwar da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa ya fitar, ya ce an kama mutanen ne bayan samun sahihan bayanan sirri da gudanar da samame.

Wadanda aka kama sun hada da Umar Auwalu, dan shekara 23 daga Sabuwar Gandu; Isyaku Yakubu (Chebe), dan shekara 40 daga Sagagi; da Yakubu Abdulaziz (Wawo), dan shekara 21 daga Sabon Gida Sharada.

Yan sandan Kano sun kama wadanda suka amsa kashe wata baiwar Allah da yaranta
Kwamishinan yan sandan Kano, Ibrahim Bakori Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Rundunar ta ce za ta bibiyi lamarin, a fadada bincike har sai an gurfanar da su a gaban kotu domin a yi hukunci dai-dai da laifin da aka aikata.

4. Ma’aikatar shari’a

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta bayyana cewa ba za a yi wata-wata ba wajen shari’ar mutanen da ake zargi da kisan mutane bakwai a Kano.

Kakakin kotunan jihar, Baba Jibo Ibrahim, ya ce wannan mummunan kisa ya girgiza zukatan jama’a, kuma gwamnati za ta bi hakkin Fatima Abubakar da ’ya’yanta har sai an tabbatar da adalci.

Sai dai ya roki ɓangaren zartarwa da su tabbatar an aiwatar da duk wani hukunci da kotunan jihar za su yanke a kan irin wadannan al'amura na rashin imani.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mutum 3 da ake zargi da kashe matar aure da yaranta 6 a Kano

Kano: Bata-gari sun kashe uwa da yaranta

A baya, kun ji cewa mazauna unguwar Dorayi Chiranci a Kano sun shiga tsahin hankali da firgici bayan kisan gilla da aka yi wa wata matar aure da 'ya'yanta shida.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu tsageru sun kashe matar da dukkanin yaran, sannan suka jefa jaririnta cikin wata rijiya a harabar gidan su ranar Asabar. Mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin abin firgici da ban tsoro, inda suka nuna alhini da fargaba kan asarar rayukan da aka yi da tsakar ranar Allah.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng