Ana Tuhumar Gwamna Mai Ci a gaban EFCC kan Bacewar Naira Biliyan 30

Ana Tuhumar Gwamna Mai Ci a gaban EFCC kan Bacewar Naira Biliyan 30

  • Kungiyar HEDA ta kai karar Gwamna Seyi Makinde gaban hukumar EFCC kan zargin karkatar da Naira biliyan 30 na tallafin Bodija
  • Gwamnatin Jihar Oyo ta dage kan cewa kudaden suna nan daram ba a taba su ba yayin da take jiran karin kudade daga tarayya
  • Masu sharhi na ganin wannan takun saka yana da alaka da siyasar 2027 dake karatowa yayin da HEDA ke son EFCC ta yi bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna HEDA, ta shigar da ƙarar gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, gaban hukumar EFCC kan zargin karkatar da kuɗi.

Ƙungiyar tana tuhumar gwamnatin jihar da rashin bayyana gaskiyar yadda aka batar da Naira biliyan 30 da gwamnatin tarayya ta bayar bayan waki'ar Bodija.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Kotu ta tura tsohon shugaban kasa gidan yari, zai yi zaman shekaru 5 a Korea

An kai koken gwamnan Oyo gaban EFCC kan zargin karkatar da N30bn.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde zaune a wurin wani taro a Ibadan. Hoto: @seyimakinde
Source: Facebook

Ana zargin gwamna da karkatar da N30bn

Shugaban ƙungiyar, Mista Olanrewaju Suraju, ya aika da wasiƙar koken zuwa ga shugaban hukumar EFCC, inda ya buƙaci a gudanar da bincike kan waɗannan kuɗaɗe, in ji rahoton Punch

Ƙungiyar HEDA ta bayyana damuwarta cewa Naira biliyan 4.5 kawai aka yi amfani da su wajen biyan diyya, yayin da sauran Naira biliyan 30 suka yi batan dabo.

A cikin takardar ƙarar mai kwanan wata 5 ga Janairu, 2026, ƙungiyar ta ce akwai alamun rashin gaskiya da cin amanar al'umma a cikin wannan lamari.

Wannan dambarwa ta fara ne bayan tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi zargin cewa gwamnatin tarayyabbOyo tana nan daram kan bayananta na baya, kuma mun san cewa shekarar 2026 lokaci ne na shirye-shiryen babban zaɓen 2027."

Gwamnatin Oyo ta karyata zargin cewa gwamna ya karkatar da N30bn
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a dakin taron gwamnonin PDP da aka gudanar a Zamfara. Hoto: @seyimakinde
Source: Twitter

Bukatar bincike da kuma kariyar gwamna

Ƙungiyar HEDA ta yi zargin cewa an ajiye kuɗaɗen ne a wani babban banki domin su tara kudin ruwa na tsawon shekara guda ba tare da an sani ba.

Kara karanta wannan

Kano da wasu jihohin Najeriya 4 da siyasarsu ke ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027

Ƙungiyar ta buƙaci EFCC ta tursasa wa gwamnatin Jihar Oyo ta fito fili ta yi bayanin yadda aka sarrafa kuɗaɗen tallafin da aka karɓa daga tarayya.

Kodayake sashe na 308 na kundin tsarin mulki ya ba gwamna kariya daga gurfanarwa, HEDA ta ce hakan ba zai hana a gudanar da bincike akansa ba.

Ana so Makinde ya nemi kujerar Tinubu

A wani labari, mun ruwaito cewa, bayan PDP ta ware tikitin takarar shugaban kasa ga Kudancin Najeriya, an fara nuna wanda ya dace jam'iyyar ta ba takararta.

Wani jigon PDP a jihar Oyo, Femi Babalola ya bayyana Gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya fi cancanta ya kare martabar PDP a babban zaben 2027.

Babalola ya ce Makinde na da duk abin da ake bukata don gyara kura-kuran da APC ke yi, duba da irin nasarorin da ya samu a duka fannoni a jihar Oyo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com