Gwamnatin jihar Oyo ta rufe Kasuwar Badija yayin da 'Yan sanda da Mahauta suka yi arangama

Gwamnatin jihar Oyo ta rufe Kasuwar Badija yayin da 'Yan sanda da Mahauta suka yi arangama

A ranar Alhamis ta yau ne gwamnatin jihar Oyo karkashin jagorancin gwamna Abiola Ajimobi, ta rufe babbar Kasuwar nan ta Bodija dake birnin Ibadan yayin da jami'an 'yan sanda da Mahauta suka yi artabu kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana.

Kamar yadda shafin gwamnatin jihar na dandalin sada zumuntar twitter ya bayyana, an rufe wannan kasuwa ne yayin da sautin harbin bindiga ya tashi sakamakon arangama tsakanin jami'ai da mahauta.

Gwamnatin jihar ta rufe kasuwar ta Bodija saboda dalilai na tsaro da kiyaye salwantar rayuka da dukiya kamar yadda Shugaban wannan gunduma ta Aare Laatosa, Adekunle Oladeji ya bayyana.

Gwamnatin jihar Oyo ta rufe Kasuwar Badija yayin da 'Yan sanda da Mahauta suka yi arangama
Gwamnatin jihar Oyo ta rufe Kasuwar Badija yayin da 'Yan sanda da Mahauta suka yi arangama

Hakazalika gwamnatin jihar ta dakatar da ta duk wata gudanarwa a kasuwar domin dakila ci gaba da ta'azzarar rikicin tsakanin jami'an da mahauta da ka iya yaduwa zuwa wasu sassa na jihar.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin jihar ta bayar da umarni ga Mahautan akan su sauya sheka zuwa wata sabuwar Kara inda suka nuna rashin amincewar su akan wannan umarni.

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace wani Fuloti na N325.4m mallakin Tsohuwar Ministan man Fetur, Diezani

A ranar Talatar da ta gabata ne Mahautan suka gudanar da zanga-zanga a sakateriyar gwamnatin jihar dake birnin Ibadan sakamakon aikin rusau da gwamnatin jihar ta aiwatar a kasuwar su ta Kara a karshen makon da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa, rikicin ya barke ne yayin da wasu mahauta suka zargi shugabannin su da goyon bayan gwamnatin dangane da kudirin akan su kauracewa tsohuwar kasuwar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng