Ma'aikatar Shari'a: Abin da za Mu Yi game da Kashe Fatima da Yaranta 6 a Kano
- Ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta yi alƙawarin bin diddigin shari’ar kisan Fatima Abubakar da yaranta shida har sai an tabbatar da adalci
- Kakakin kotunan Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya ce ba za a yi jinkiri wajen shari’ar wadanda ake zargi ba, sai dai ya mika roko ga bangaren zartarwa
- Baba Jibo Ibrahim ya ce akwai bukatar bangaren zartarwa da ya gaggauta zartar da duk wani hukunci da kotu ta yanke ba tare da ɓata lokaci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta yi bayani kan kisan rashin imani da ya auku a unguwar Chiranchi da ke Dorayi a Kano.
Wasu bata-gari uku sun shiga gidan Fatima Abubakar suka kashe ta tare da yaranta shida baki ɗaya a ranar Asabar 17 ga watan Janairu, 2026.

Source: Facebook
Wannan bayani na zuwa ne bayan bidiyon da Freedom Radio ta wallafa a shafinta na Facebook, inda Kakakin kotunan Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya jaddada cewa ba za a yi wata-wata ba wajen shari’ar wadanda ake zargi da kisan gillar.
Ma’aikatar shari’a za ta bi hakkin Fatima, yaranta
Baba Jibo Ibrahim ya bayyana cewa wannan mummunan kisa ya girgiza zukatan jama’a, musamman masu sauran burbushin imani a zukatansu.
A cewarsa, lamarin ya shafi al’umma baki ɗaya, tare da haifar da fargaba da firgici a al'ummar da ke Kano, Arewa da sauran sassan Najeriya.
A kalamansa:
“Abu ne wanda ya taba zukatan duk masu burbushin imani a zukatansu, abin ya taba su. Kiranmu ga bangaren zartarwa daga lokacin da aka ce an samu kammaluwar hukunci da kotuna suka yi da a gaggauta zartar da irin wannan hukunci da kotu ta yi ba tare da jinkiri ba.”
Ya bayyana cewa tabbatar da hukuncin da kotu ta yanke zai taimaka wajen kwantar da hankalin jama’a daga irin matsin zuciya da suke ciki sakamakon wannan ta’addanci.
Baba Jibo ya tabbatar da cewa ma’aikatar shari’a za ta tabbatar an bi hakkin jinin Fatima Abubakar da dukkannin yaranta, tare da tabbatar da cewa shari’ar za ta gudana bisa gaskiya da adalci.
Za mu tabbatar da adalci – Ma’aikatar shari’at Kano
Kakakin kotunan ya jaddada cewa duk wata kotu da za a kai wannan mummunan kisa, za a yi adalci ba tare da kasa a gwiwa ba.
Ya ce ma’aikatar shari’a za ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan duk wanda aka samu da laifi.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Muna amfani da wannan dama wajen mika ta’aziyyarmu ga al’ummar duniya da ita kanta gwamnatin jihar Kano da ‘yan uwan wadanda aka kashe bisa ga wannan ta’addanci da aka kashe.”
Ya kuma tuna yadda har yanzu ake ci gaba da shari’a kan kisan wata karamar yarinya a Kano mai suna Hanifa Abubakar, inda ya ce shari’ar na nan tana tafiya duk da kalubalen da ake fuskanta.

Kara karanta wannan
"Ba za mu lamunta ba:" Gwamna Abba ya yi alkawarin nema wa fatima da yaranta adalci
Ya bayyana cewa daga bangaren kotu, ana kokarin yin adalci a dukkannin shari’o’in da ke gabanta, domin ana yanke hukunci bisa tanadin doka.
Gwamnati ta yi magana kan kisan Fatima
A wabi labarin, mun wallafa cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar baƙin ciki da alhini kan kisan gilla da aka yi wa wata mata ’yar Kano, Fatima Abubakar, tare da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi.
Gwamnan ya bayyana wannan lamari a matsayin mummunan aiki na rashin imani, marar dalili, kuma babban cin mutunci ga darajar ɗan Adam, yana mai jaddada cewa ba za a taɓa amincewa da irin wannan danyen aiki ba.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Asabar, bayan rasuwar bayin Allah da ya tayar da hankalin jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

