Ribadu Ya Tafka Babban Rashi, Allah Ya Karbi Ran Mahaifiyarsa Tana da Shekaru 86

Ribadu Ya Tafka Babban Rashi, Allah Ya Karbi Ran Mahaifiyarsa Tana da Shekaru 86

  • An shiga jimami bayan sanar da rasuwar mahaifiyar Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu bayan ta sha fama da jinya
  • Marigayiya Hajiya Aisha Mamma ta rasu da safiyar Litinin 19 ga watan Janairun 2026 tana da shekaru 86
  • Marigayiyar ita ce kuma mahaifiyar Sarkin Fufore a Jihar Adamawa, Mai Martaba Sani Ribadu, inda manyan mutane suka fara mika ta’aziyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rahotannin da muke samu sun tabbatar da rasuwar mahaifiyar mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

An ce Hajiya Aisha Mamma ta rasu da safiyar Litinin 19 ga watan Janairun 2025 tana da shekaru 86 a duniya bayan fama da jinya.

An sanar da rasuwar mahaifiyar Nuhu Ribadu
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu. Hoto: Nuhu Ribadu.
Source: Facebook

Marigayiyar, wadda aka fi sani da Hajja Mamma, ita ce kuma mahaifiyar Sarkin Fufore a Jihar Adamawa, Mai Martaba Sani Ribadu, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

APC ta fito karara ta yaba wa Atiku duk da adawar da ya ke da Tinubu

Tinubu ya jajanta wa Nuhu Ribadu

Ko a shekarar 2024 ma, Ribadu ya yi rashin daya daga cikin yan uwansa wanda ya yi bankwana da duniya a jihar Adamawa.

Ɗan uwan mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya koma ga mahaliccinsa bayan ya yi rashin lafiya na tsawon lokaci.

Salihu Ahmadu Ribadu ya yi bankwana da duniya ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayun 2024 a birnin Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika da tawaga ta musamman domin yi wa Nuhu Ribadu ta'aziyyar wannan babban rashin da ya yi.

Nuhu Ribadu ya yi rashin mahaifiyarsa

Daya daga cikin mutanen farko da suka mika ta’aziyya ga iyalan Ribadu ita ce Sanata Aishatu Dahiru Ahmed, wadda aka fi sani da Binani.

Sanata Binani ta bayyana marigayiyar a matsayin “uwa ga kowa,” tana cewa hikimarta da addu’o’inta sun zama kariya ga yara da al’umma.

Kara karanta wannan

Idan Abba ya koma APC, waye Sarkin Kano? 'Yan majalisa sun yi karin haske

Ta ce:

“Mun rasa ginshikin zaman lafiya, marigayiyar ta kasance mai hakuri, tawali’u da tsoron Allah."
Nuhu Ribadu ya yi rashin mahaifiyarsa
Taswirar jihar Adamawa da Nuhu Ribadu ya fito. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka gudanar da sallar jana'izar marigayiyar

Ta’aziyyar jana’izar, wadda aka gudanar bisa koyarwar Musulunci, ta samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin tsaro da sarakuna daga Arewa maso Gabas.

Rahoton PM News ya ce mutane da dama da suka halarci sallar jana'izar sun yi jinamin rasuwar dattijuwar inda suke bayyana gudunmawar da ta bayar.

Mafi yawa sun yaba da riƙon addininta da kuma zama uwa ga iyalanta da tabbatar da zaman lafiya a tsakani wanda ya taka rawa wurin daga darajarsu.

Ribadu ya magantu kan yaki da ta'addanci

Mun ba ku labarin cewa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce ƙasashen duniya na haɗa kai da Najeriya wajen ceto ɗaliban da aka sace.

Ya ziyarci makarantar St Mary da ke Papairi, inda aka sace malamai da ɗalibai 265, ya kuma miƙa saƙon shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Malam Nuhu Ribadu ya ce gwamnatin tarayya ta ɗauki alhakin lamarin tare da alƙawarin ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin da ceto daliban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.