Masarauta a Kano ta Haramta Kiɗa da Wakokin Turawa a Taron Bukukuwa
- Majalisar Masarautar Rano a jihar Kano ta bayyana haramta amfani da kidin turawa a yayin bukukuwa a yankin
- Masarautar ta bayyana mai da hankali sosai kan yadda tarbiyyar matasa ke kasancewa a wannan karni
- An kuma samu goyon bayan jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a wannan aiki na gyaran tarbiyyar matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Rano, Jihar Kano - Majalisar Masarautar Rano a Jihar Kano ta sanya dokar haramta amfani da kiɗan da wakokin turawa a bukukuwan aure da sauran tarukan jama’a a fadin masarautar.
Masarautar ta dauki wannan matakin ne duba da illolin da hakan ke haifarwa ga tarbiyya da ɗabi’un al’ummar yankin.
Wazirin Rano, Alaramma Kabir Sani, ne ya bayyana wannan matsaya yayin wani shirin wayar da kan matasa da Majalisar Shari’ar Musulunci ta Karamar Hukumar Rano ta shirya.

Source: Original
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an gudanar da taron ne a fadar Sarkin Rano, inda manyan jami’ai da malamai suka halarta.
Gyaran tarbiyya aka sa a gaba a Rano
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na yankin Rano, Abdullahi Musa Gyadi Gyadi, ya fitar a ranar Asabar, an bayyana cewa Wazirin ya jaddada muhimmancin tarbiyya nagari ga matasa domin kare al’umma daga lalacewar tarbiyya.
Alaramma Kabir Sani ya ce hukumomin Karamar Hukumar Rano da Majalisar Masarautar Rano sun cimma matsaya guda kan wannan haramci, tare da cikakken goyon bayan sauran hukumomin tsaro.
Ya bayyana cewa an dauki matakin ne bayan la’akari da mummunar tasirin da kiɗan DJ na salon Turawa ke yi ga tarbiyyar matasa da gina halayen al’umma, The Sun ta ruwaito.
Wayoyin hannu sun bata tarbiyyar matasa
Wazirin ya kuma nuna damuwa kan yadda matasa ke yin amfani da wayoyin hannu ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa hakan na kara jefa su cikin dabi’u marasa kyau.
Ya bukaci iyaye da shugabanni da su saka ido sosai kan tarbiyyar ‘ya’yansu, tare da koyar da su daraja da halaye na addini da al’ada tun suna kanana.

Kara karanta wannan
"Ba za mu lamunta ba:" Gwamna Abba ya yi alkawarin nema wa fatima da yaranta adalci

Source: Getty Images
A nasa jawabin, Hakimin Rano, Adda’u Isah, wanda wakilinsa Balarabe Adda’u Isah Rano ya wakilta, ya yaba wa Majalisar Shari’ar Musulunci ta Karamar Hukumar Rano bisa wannan shiri na wayar da kan jama’a.
Masarautar Rano ta ba da goyon baya
Ya tabbatar da cewa masarautar za ta ba da cikakken goyon baya ga duk wani shiri ko aiki da ke da nufin karfafa koyarwar Musulunci da kyawawan dabi’u a yankin.
Shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Karamar Hukumar Rano, Idris Garba Rano, ya bayyana cewa wannan wa’azi da shirin fadakarwa ba zai tsaya a wuri guda ba.
Ya ce za a kai irin wannan shiri zuwa dukkan gundumomi 13 da ke karkashin majalisar domin wayar da kan matasa da iyaye.
Idris Garba Rano ya kuma yi kira ga iyaye da su dauki cikakken nauyin tarbiyyar ‘ya’yansu, yana mai jaddada cewa iyali na da muhimmiyar rawa wajen gina al’umma mai tarbiyya da tsoron Allah.
An hana Kauyawa Day a Kano
A wani labarin, Sakatare Janar na Hukumar Tace Fina-Finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa gwamnati ta dakatar da duk wasu bukukuwa da ake kira Kauyawa Day.
A wata sanarwa da ya fitar bayan taron gudanarwa na hukumar tace fina-finai, y ace, hukumar ta rufe dukkan cibiyoyin shirya bukukuwa har zuwa wani lokaci.
Jihar Kano na daga jihohin da ake yawan samun daukar matakai kan matasa, musamman daga hukumomi da masarautun gargajiya.
Asali: Legit.ng

