Tashin Hankali: An Yi Wa Wata Matar Aure da 'Ya'yanta 3 Kisan Rashin Imani a Kano
- Wasu tsageru da ba a gano ko su waye ba sun shiga har gida, sun kashe matar aure da 'ya'yanta uku a cikin birnin Kano
- Wannan mummunan al'amari ya auku ne a unguwar Dorayi Chiranci, kuma an ce maharan sun jefa karamin jaririn matar a cikin rijiya
- Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar yan sanda, amma mazauna Dorayi sun ce lamarin ya tada masu hankali matuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Mazauna unguwar Dorayi Chiranci a cikin birnin Kano sun shiga tsahin hankali da firgici bayan kisan rashin imani da aka yi wa wata matar aure da 'yayanta.
Rahotanni sun nuna cewa wasu tsageru da ba a gane ko su waye ba kawo yanzu, sun kashe matar da 'ya'yanta uku, sanann suka jefa jaririnta cikin wata rijiya a cikin gidansu.

Source: Original
Jaridar Tribune Nigeria ta rahoto cewa mazauna yankin sun ce har yanzu ba a gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki ba, yayin da jami’an tsaro suka fara bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.
Yadda aka kashe mace da yaranta a Kano
A cewar mazauna yankin, maharan sun kashe matar da ’ya’yanta uku, sannan suka jefa jaririnta cikin rijiya da ke cikin harabar gidan su.
Har yanzu ba a san ainihin lokacin da lamarin ya faru ba, haka kuma ba a gano dalilin kashe su ba, kamar yadda Punch ta kawo.
Mutanen yankin sun bayyana lamarin a matsayin abin firgici da ban tsoro, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba, inda suka nuna alhini da fargaba kan asarar rayukan da aka yi.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara yawan sintiri a yankin tare da tabbatar da cewa an kama waɗanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukuncin abin da suka aikata.
Mazauna Dorayi sun dauki mataki
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Talata da ta gabata, aka fara zaman fargaba da dar-dar a unguwar Dorayi Chiranci, inda mazauna yankin suka ɗauki matakan kariya sakamakon fargabar tsaro.
Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano bai yi nasara ba, domin jami'in hulda da jama'a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai samu damar amsa kiran waya ba.

Source: Twitter
Har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar 'yan sanda ko wata hukuma, sai dai mutanen Dorayi na ci gaba da kira da a dauki matakin kama masu hannu a lamarin.
An tsinci gawarwakin yan gida daya a Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa an gano gawarwakin mutane shida 'yan gida daya a gidansu da ke kauyen Ogale Eleme, a Karamar Hukumar Eleme ta Jihar Rivers.
Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa hayakin janareta ne ake zargin ya yi ajalin mutanen.
Kwamishinan 'yan sandan Rivers, Olugbenga Adepoju, ya ja hankalin mutane su guji kunna janareta a wuraren da suke kwanciya barci don kauce wa matsala.
Asali: Legit.ng

