Shugaban Kasa Tinubu Zai San Hukuncin Aikinsa bayan Shigar da Shi Kara a Kotu
- Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da aka shigar kan yadda aka aiwatar da dokar-ta-baci a Jihar Rivers zuwa ranar 9, Maris, 2026
- Ƙungiyar CSOCLC ta ƙalubalanci ikon Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cire zaɓaɓɓun shugabanni da kafa gwamnatin rikon-kwarya
- Rahotanni sun nuna cewa lauyoyi biyu sun yi muhawara a kotun game da tanadin kundin tsarin mulki da kuma tasirin tsohuwar dokar ta-baci ta 1962
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kotun Tarayya da ke Abuja ta saka ranar 9, Maris, 2026 domin yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar domin ƙalubalantar yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da dokar-ta-baci a Jihar Rivers.
Ƙarar ta shafi matakan da suka biyo bayan ayyana dokar-ta-baci a jihar a shekarar 2025, ciki har da dakatar da zaɓaɓɓun shugabannin zartarwa da na majalisa da kuma kafa shugabanci na wucin-gadi.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa al’amarin ya sake tayar da muhawara kan iyakar ikon shugaban ƙasa a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, musamman sashe na 305.
Yadda aka yi shari'ar Bola Tinubu a kotu
Mai shari’a James Omotosho ne ya ɗage sauraron shari’ar a ranar Juma’a bayan dukkan ɓangarori sun kammala gabatar da hujjoji kan sabon ƙudiri da aka shigar.
Ƙarar ta fito daga ƙungiyar CSOCLC, wadda ta shigar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Tarayyar Najeriya, Antoni-Janar na Tarayya, Jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, INEC da kuma Gwamna Sir Siminalayi Fubara a kotu.
Rahoton jaridar the Sun ya nuna cewa kungiyar ta ce matakan da aka ɗauka bayan ayyana dokar-ta-baci sun saɓa wa kundin tsarin mulki.
Hujjar ƙungiyar CSOCLC kan Tinubu
Lauyan CSOCLC, Nnamdi Nwokocha-Ahaaiwe, ya shaida wa kotu cewa duk da kundin tsarin mulki ya bai wa shugaban ƙasa ikon ayyana dokar-ta-baci, bai ba shi ikon cire ko dakatar da zaɓaɓɓun shugabannin zartarwa da na majalisa ba.
Ya jaddada cewa sashe na 305 na kundin tsarin mulki ya fayyace iyakar ikon shugaban ƙasa, kuma babu wani tanadi da ya ba shi damar kafa shugabanci na wucin-gadi a jihar.
Ahaaiwe ya ce tsohuwar dokar 1962, wadda wasu shari’o'i suka dogara da ita a baya, doka ce da ba a amfani da ita, kuma an cire ta daga kundin dokoki kafin kundin tsarin mulki na 1999 ya fara aiki.

Source: Facebook
A nasa ɓangaren, lauya mai kare gwamnati, Akinsola Olujimi, ya roƙi kotu da ta yi watsi da ƙarar gaba ɗaya tare da ɗaura wa masu shigar da ita tara.
Bayan kammala sauraron dukkan hujjoji, kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 9, Maris, 2026 domin yanke hukunci a kan karar da aka shigar.
Ana shirin tsige Gwamna Fubara a Rivers
A wani labarin, mun kawo muku cewa majalisar dokokin jihar Rivers ta fara sabon yunkurin tsige gwama Siminalayi Fubara daga mulki.
Hakan na zuwa ne bayan sabanin da suka samu da shi duk da shugaba Bola Tinubu ya musu sulhu a kwanakin baya da suka kai ruwa rana.
Rikicin siyasar Rivers da ya samo asali kan sabanin gwamna Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike ya kai ga ayyana dokar ta baci a 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

