Jigo a Kwankwasiyya Ya Fadi Wanda Kwankwaso Zai Tsayar da Zai Kada Gwamna Abba

Jigo a Kwankwasiyya Ya Fadi Wanda Kwankwaso Zai Tsayar da Zai Kada Gwamna Abba

  • Jigo a Kwankwasiyya, Saddam Sani Umar, ya fito ya yi magana kan shirin sauya shekar Gwamna Abba Kabir na Kano zuwa jam'iyyar APC
  • Saddam Sani Umar ya bayyana cewa Kwankwaso da Kwankwasiyya ba za su yi asara ba don gwamnan ya koma APC
  • Ya bayyana cewa a yadda siyasar Kano take, mutane na yi wa madugun Kwankwasiyya kallon jagoran talakawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Jigo a Kwankwasiyya, Saddam Sani Umar, ya yi tsokaci kan shirin sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC.

Saddam Sani Umar wanda shi ne jami’in kula da walwala na mambobin Kwankwasiyya a jihar Kano, ya bayyana cewa ba a cin amanar Kwankwaso a zauna lafiya.

Jigo a Kwankwasiyya ya ce Kwankwaso ba zai yi asara ba kan sauya shekar Gwamna Abba
Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Saddam Sani Umar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust ta yi da shi.

Kara karanta wannan

Sauya shekar Abba: NNPP ta ce lokaci bai ƙure ba, tana fatan Gwamna zai hakura

Kwankwaso ba zai yi asara ba

Jigon na Kwankwasiyya ya bayyana cewa bai yarda da batun cewa Kwankwaso da Kwankwasiyya za su yi asara ba idan Gwamna Abba ya koma jam'iyyar APC.

“Ban yarda da hakan ba. Kwankwaso shi ne jagoran wannan tafiya a faɗin Najeriya baki ɗaya, ba a Kano kaɗai ba. A ce shi ne zai yi asara, hakan na nuna rashin fahimtar gaskiya."
"Ko da jam’iyyar siyasa ta ce tana da karfi, dukkaninsu suna neman Kwankwaso ne. Shi kaɗai ne jagora a wannan kasa da ke tsayawa tsayin daka wajen kare talakawa.”

- Saddam Sani Umar

Ba a cin amanar Kwankwaso a zauna lafiya

Jigon na Kwankwasiyya ya bayyana cewa duk wanda ya ci amanar Kwankwaso, bai ganin da kyau a tafiyarsa.

“Cin amanar Kwankwaso ba ya karewa da kyau, tarihi ya tabbatar da hakan. Ku kalli gwamnatin da ta gabata. Ganduje ya ci amanar Kwankwaso, daga karshe shi ne ya yi asara."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta hango lam'a a kalaman Kwankwaso na tilasta wa masoyansa koma wa APC

"A shekarar 2019 sun sha kaye a zaɓe, ba don wancan sakamakon ‘inconclusive’ mai ce-ce-ku-ce ba. A 2023 kuma, ko da Kwankwaso bai da ko kansila ɗaya a gwamnati, shi kaɗai ya kawo ‘Abba Gida Gida’.”
“Abba bai taɓa tsayawa takara a rayuwarsa ba, ko kansila ma bai taɓa nema ba. Ya yi aiki a matsayin mataimaki na musamman (PA) ga Kwankwaso sama da shekaru 30."
"Kwankwaso ne ya ɗaga shi ya zama kwamishina, daga nan kuma ya zama gwamna. Don haka tunanin cewa Kwankwaso zai yi asara a yanzu kuskure ne.”

- Saddam Sani Umar

Jigo a Kwankwasiyya ya ce Kwankwaso na da mabiya a Kano
Jigo a Kwankwasiyya a Kano, Saddam Sani Umar Hoto: Hon Saddam Sani Umar
Source: Facebook

Waye zai kada Gwamna Abba?

Da aka tambaye shi ko yana nufin APC da Gwamna Abba Yusuf ne za su yi asara a karshe, sai ya kada baki ya ce:

“Eh, haka nake nufi. Su ne za su yi asara a Kano. Idan lokaci ya yi, jama’a za su fito kwarai su kaɗa ƙuri’a ga duk wanda Kwankwaso ya zaɓa."
"A Kano, idan Kwankwaso ya zaɓi kare, mutane za su zaɓe shi, domin sun amince da shi a matsayin jagora da ke tsayawa tare da mutanensa.”

- Saddam Sani Umar

Kara karanta wannan

An zo wajen: Kwankwaso ya kafa sharadin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Fatan da NNPP ke yi kan Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta yi magana kan shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa har yanzu tana fatan Gwamna Abba Kabir Yusuf zai fasa sauya sheka zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Ta bayyana cewa da tana fatan Gwamna Abba Kabir Yusuf zai iya fasa sauya sheka, babu wanda zai masa dole ya ci gaba da zama a NNPP idan ba ya so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng