Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari kan Ƴan Sanda, An Rasa Rayuka

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari kan Ƴan Sanda, An Rasa Rayuka

  • 'Yan bindiga da ake zargin mayakan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun kashe yan sanda biyu tare da kona motar sintiri a garin Enugu
  • Kwamishinan 'yan sanda ya bada umarnin kamo maharan da suka tsere da raunukan harbin bindiga bayan musayar wuta da jami'ai
  • Wannan shi ne hari na biyu makamancinsa a cikin kasa da wata guda da 'yan bindiga suka kai kan shingen binciken 'yan sanda a Enugu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu - Rundunar ƴan sandan Jihar Enugu ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun kai hari wani shingen bincikenta da ke titin Agbani, inda suka kashe jami’ai biyu tare da ƙona motar sintiri.

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar, SP Daniel Ndukwe, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Alhamis, 15 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Enugu, sun kashe jami'ai biyu.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun fito suna sintiri a babban titi. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Enugu

Ana zargin mambobin ƙungiyar IPOB da reshenta na ESN ne suka buɗe wa dakarun ƴan sanda na sashen kai daukin gaggawa wuta, in ji rahoton Punch.

A cewar sanarwar, jami'an ƴan sandan sun mayar da martanin wuta cikin gaggawa, wanda hakan ya tilasta wa maharan tserewa da raunukan harbin bindiga a jikinsu yayin fafatawar.

Sai dai kash, motar aiki ta ƴan sanda ta kama da wuta bayan an harbe ta, sannan jami'ai biyu sun sami munanan raunukan harbi wadanda suka yi sanadin rasa rayukansu.

Umarnin bincike da kamo maharan

An ce an garzaya da jami'an asibiti domin ba su taimakon gaggawa, amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa sakamakon raunukan da suka samu, in ji Sahara Reporters.

Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Enugu, Mamman Bitrus Giwa, ya ba da umarnin ƙarfafa bincike tare da tura dakarun sirri da na yaƙi domin bin sawun maharan da suka tsere.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke mutane 3 dauke da kayayyakin hada bama bamai a Daura

Rundunar ta yi nasarar gano wata mota ƙirar Lexus 330 wadda maharan suka yi amfani da ita yayin harin, wadda aka tsince ta cike da ramin harsashi bayan musayar wutar.

Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin gaggauta kamo 'yan ta'addar da suka farmaki jami'ansu
Taswirar jihar Enugu, inda 'yan bindiga suka kashe jami'an 'yan sanda biyu. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Makamancin harin da ya faru a baya

Wannan hari na zuwa ne makonni kaɗan bayan wani makamancinsa da ya faru ranar 27 ga Disamba, 2025, a kan titin Zik Avenue a cikin birnin na Enugu.

A wancan harin ma, an kashe jami'ai biyu masu suna Insfeta Valentine Iheme da Insfeta Anayo Ede, sannan aka ƙona motar su tare da sace bindigogi ƙirar AK-47 guda uku.

Hukumar ƴan sanda ta jaddada cewa ba za ta huta ba har sai ta tabbatar da cewa masu tada ƙayar baya da ke addabar jihar ba su tsira daga fuskantar shari'a ba.

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sandan Enugu

A wani labarin ma, Legit Hausa ta rahoto cewa, wasu ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari kan ƴan sanda a garin Achị, ƙaramar hukumar Oji River a Enugu.

Ƴan bindigan sun kashe ƴan sanda uku tare da wani farar hula guda ɗaya a ranar Talata, 15 ga watan Afrilu, 2025 kamar yadda rundunar ta sanar.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne a wani shingen bincike da ke kusa da kasuwar Ozudaa, wadda ta shahara a cikin garin Achi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com