Ana Zargin Gwamna Ya Handame Kudaden Kananan Hukumomi, ALGON Ta Yi Bayani

Ana Zargin Gwamna Ya Handame Kudaden Kananan Hukumomi, ALGON Ta Yi Bayani

  • Shugabannin ƙananan hukumomin Abia sun musanta zargin cewa Gwamna Alex Otti yana karkatar da kuɗaɗen su da aka turo daga tarayya
  • ALGON ta bayyana cewa har yanzu ana amfani da asusun JAAC wajen raba kuɗaɗe tsakanin jiha da kananan hukumomi idan FAAC ta tura masu
  • Ƙungiyar ALGON ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da mulkin Gwamna Otti sakamakon ayyukan raya ƙasa da biyan albashin ma'aikata da ya ke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abia - Ƙungiyar ALGON reshen Jihar Abia, ta musanta raɗe-raɗin da ake yi na cewa ana karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar ko kuma ana yin sama da faɗi da su.

Shugaban ALGON na jihar kuma ciyaman din Isuikwuato, Hon. Chinedu Ekeke, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai ranar Juma'a, 16 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Bayan Sule Lamido, Kotun Koli ta yi hukunci kan zargin 'dansa da cin hanci

ALGON ta wanke gwamnan Abia daga zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi
Gwamnan Abia, Alex Otti yana daga wa masoyansa hannu a taron kaddamar da ginin titin Ntigha-Mbawsi-Umuala. Hoto: @alexottiofr
Source: Twitter

Matsayar ALGON kan 'yancin kananan hukumomi

Ekeke ya jaddada cewa babu wani kuɗi da gwamnatin jiha ke dannewa, inda ya ce har yanzu tsarin raba kuɗaɗen yana tafiya ne ta asusun bai-ɗaya na jiha da ƙananan hukumomi (JAAC), in ji rahoton Punch.

Yayin da aka tambaye shi game da hukuncin Kotun Ƙoli na ba wa ƙananan hukumomi 'yancin gashin kai, Ekeke ya bayyana cewa gwamnatin tarayya har yanzu tana kokarin lalubo hanyar da za a bi wajen aiwatar da hakan.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu, kuɗaɗe ba sa zuwa kai-tsaye daga tarayya zuwa ƙananan hukumomi, suna bi ta asusun JAAC ne.

Martani ga masu sukar Gwamna Otti

Shugaban ALGON ya ce Gwamna Alex Otti yana bai wa ƙananan hukumomin duk tallafin da suke buƙata don gudanar da ayyukansu.

Hakazalika, Ekeke ya jaddada cewa akwai kyakkyawar alaƙa da haɗin kai tsakanin gwamnatin Alex Otti da na kananan hukumomi a jihar.

Kara karanta wannan

ADC: Momodu ya kare Atiku kan zargin shirin amfani da kuɗi wajen sayen takara

Ƙungiyar ta ALGON ta soki wasu tsofaffin gwamnoni da jiga-jigan siyasa waɗanda ta bayyana a matsayin "magabata da suka gaza," waɗanda ke ƙoƙarin yi wa nasarorin Gwamna Alex Otti zagon ƙasa.

ALGON ta bayyana cewa irin kalaman da suke yi kan makomar siyasar gwamnan ba su da tushe, in ji rahoton Daily Post.

Ciyamomin Abia sun kada kuri'ar amincewa da mulkin Gwamna Alex Otti.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya na jawabi ga 'yan jarida a gidan gwamnati, Umahia. Hoto: Hoto: @alexottiofr
Source: Facebook

An yaba da ayyukan Gwamna Alex Otti

A cewar ƙungiyar, Otti ya nuna ƙwarewa wajen gyara da gina hanyoyi, asibitoci da makarantu a duk ƙananan hukumomi 17.

Sannan kungiyar ta ce gwamnan ya na biyan albashi da fansho a kan lokaci, gami da share tsofaffin basussukan da ya gada da kuma tafiyar da dukiyar jihar cikin gaskiya da riƙon amana.

A ƙarshe, shugabannin ƙananan hukumomin sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da Gwamna Alex Otti, suna masu cewa nasarorin da ya samu ne za su nuna makomarsa ta siyasa, ba wai kalaman ƴan adawa ba.

Gwamna Otti ya cika baki kan tazarce

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya yi tsokaci kan shirin da ya yi wa babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fito ya fadi gaskiya kan kudaden da ke shigowa hannun gwamnoni

Gwamna Otti ya bayyana kwarin gwiwarsa na sake lashe zabe, yana mai cewa zaben shekarar 2027 zai fi masa sauki idan aka kwatanta da zabubbukan da ya shiga a baya.

Gwamna Otti ya ce ba ya jin tsoron zaben 2027, domin nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan hawansa mulki za su taimaka masa matuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com