Kotu Ta Yi Hukunci a Karar da Gwamnatin Tarayya Ta Shigar da Sanata Natasha
- An kawo karshen shari'ar da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan
- Shari'ar ta zo karshe ne a zaman da babbar kotun tarayya ta yi a ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026 a birnin Abuja
- Tun da farko dai gwamnatin tarayya ta shigar da karar ne a shekarar 2025 kan Sanata Natasha bisa zargin bata suna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wata babbar kotun babban birnin taarayya Abuja da ke Maitama ta yi hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Kotun ta yi watsi da tuhumar laifi da gwamnatin tarayya ta shigar kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ce Mai shari’a Chizoba Orji, wadda ke jagorantar shari’ar, ta yanke hukuncin a ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
AFCON 2025: Gwamnatin tarayya ta tuna da Super Eagles bayan rashin nasara a hannun Morocco
Babbar kotun ta yi hukuncin ne bayan da gwamnatin tarayya ta shigar da sanarwar janye karar.
Lauyan Natasha ya mika bukatarsa a kotu
A zaman kotun, lauyan Sanata Natasha, West Idahosa, ya nemi kotu ta yi watsi da shari’ar bisa rokon janyewar da masu gabatar da kara suka yi.
Haka kuma ya roki kotu da ta bayar da umarnin a mayar da dukkan takardun da ke hannun kotu na wadda ake tuhuma da masu tsaya mata beli.
Lauyan gwamnatin tarayya bai yi adawa da wannan rokon da wadanda ake kara suka gabatar ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Wane hukunci kotu ta yanke?
Sakamakon haka, kotun ta yi watsi da shari’ar, inda Mai shari’a Orji ta sallami masu tsayawa sanatar beli tare da bayar da umarnin a mayar musu da dukkan takardunsu.
An gurfanar da Sanata Natasha a gaban kotun ne a watan Yuni 2025 bisa tuhume-tuhume uku da suka shafi bata suna, inda gwamnatin tarayya ta kasance mai shigar da kara.
Karar dai an shigar da ita ne a ranar 16 ga watan Mayu, 2025, ƙarƙashin lambar shari’a CR/297/25.
Sanata Natasha ta yi martani kan hukuncin
Da take mayar da martani bayan zaman kotun, Sanata Natasha ta bayyana hukuncin a matsayin tabbaci na gaskiyar matsayarta.
“Wannan sakamakon da aka samu ya tabbatar da yardar na yi ga doka da oda. Ina ci gaba da jajircewa wajen yi wa al’ummata hidima da kare hakkin dimokuraɗiyyar dukkan ’yan Najeriya."
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Source: Facebook
Ta kara da cewa hukuncin ya nuna cewa tsarin doka shi ne ginshiƙin dimokuraɗiyyar Najeriya, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da mayar da hankali kan aikinta na majalisa da hidima ga al’ummar Kogi ta Tsakiya.
Sanatar ta kuma nuna godiya ga tawagar lauyoyinta da magoya bayanta bisa goyon bayan da suka nuna mata a tsawon lokacin shari’ar.
Akpabio ya shigar da karar Sanata Natasha
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya shigar da kara kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanata Godswill Akpabio ya shigar da karar ne kan zargin bata suna a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja.
Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa shigar da karar da shugaban majalisar dattawan ya yi, zai ba ta damar tabbatar da zargin da ta yi a kansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
