Musulunci Ya Yi Rashi: ’Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini a Kaduna

Musulunci Ya Yi Rashi: ’Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini a Kaduna

  • An kashe fitaccen malamin addinin Musulunci a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna yayin da yake tattara itacen girki
  • Marigayin Alaramma Malam Bello ya rasa ransa ne duk da yarjejeniyoyin zaman lafiya da yan bindiga da aka sanar
  • Malamin ya kasance jagoran tafsirin Alƙur’ani a masallacin JIBWIS na Juma’a da ke Layin Dan’auta, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Alaramma Malam Bello, wanda ya kasance jagoran tafsirin Alƙur’ani a masallacin JIBWIS ya rasa ransa.

Lamarin ya faru ne a unguwar Layin Dan’auta a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, ya rasa ransa bayan cin karo da ‘yan bindiga.

Yan bindiga sun kashe malamin Musulunci a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna da yan bindiga ke kai hare-hare. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Bakatsine ya tabbatar da haka a shafinsa na X a daren yau Alhamis 15 ga watan Janairun shekarar 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Rashin imani: An watsa wa dan shekara 17 acid a hanyar zuwa masallaci a Adamawa

Majiyoyi sun nuna cewa an kashe malamin ne a lokacin da ya fita tattara itacen girki domin amfanin gidansa.

Lamarin ya faru ne duk da cewa a baya an sha sanar da cimma yarjejeniyoyin zaman lafiya da kokarin sulhu tsakanin al’umma da kungiyoyin ‘yan bindiga a yankin.

Mutuwar Alaramma Malam Bello ta girgiza mazauna Birnin Gwari, inda da dama ke bayyana bakin ciki da fargaba kan yadda kashe-kashe da hare-hare ke ci gaba ba tare da wani takunkumi ba.

Mazauna yankin na tambayar inda yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka sanar suka dosa, tare da masu ba da garantin sulhun da kwamitocin zaman lafiya da aka kafa, ganin yadda hare-hare da kisan jama’a ke ci gaba duk da ikirarin an samu zaman lafiya.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce lamarin ya kara tabbatar da cewa har yanzu matsalar tsaro na ci gaba a Birnin Gwari, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Al'ummar yankin sun bukaci gwamnati ta dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga hare-hare ta'addanci da ake kai wa.

Kara karanta wannan

Yaran Turji sun yi ta'asa a Sokoto bayan sakon dan ta'addan ya rikita jama'a

Jami'an tsaro sun cafke malamin Musulunci a Kaduna

Mun ba ku labarin cewa jami'an tsaro sun cafke tare da ci gaba da tsare Sheikh Sani Khalifa Zaria tsawon kwanaki 23 kan zargin alaka da shirin juyin mulki.

Iyalan malamin sun bayyana cewa kudin da aka tura masa kyauta ce ta neman addu'a daga wani soja, ba wai kudin cin amanar kasa ba.

Masu fafutuka na kiran gwamnati da ta saki malamin tunda bincike ya nuna ba shi da masaniya kan wani shirin hambarar da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.