Badakalar N1.35bn: Sule Lamido, Ɗansa Za Su San Makomarsu, Kotun Koli Za Ta Yi Hukunci
- Kotun Koli za ta yanke hukunci kan shari’ar almundahana ₦1.35bn da ta shafi tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido
- EFCC ta kai ƙara Kotun Koli ne bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sallami Lamido da ’ya’yansa, tana cewa hujjoji sun nuna akwai shari’a a kansu
- Ana zargin Lamido da karɓar kuɗin kwangila a matsayin rashawa lokacin mulkinsa daga 2007 zuwa 2015
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kotun Koli za ta yanke hukunci kan shari’ar almundahana ta ₦1.35bn da ta shafi tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.
Shari’ar ta kuma haɗa da ’ya’yansa biyu, Mustapha Lamido da Aminu Lamido, waɗanda aka jima ana gurfanarwa a gaban kotu kan zargin taba kuɗaɗen haram.

Source: Twitter
Kotun koli za ta duba shari'ar Sule Lamido
Hukumar EFCC ta sanar da hakan ne ta shafinta na Facebook a ranar Alhamis 15 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Zafin siyasa bai hana aiki: Abba ya fadi shirin gwamnati a kan matasa 50, 000 a Kano
Za a yanke hukuncin ne a gobe Juma'a 16 ga watan Janairun 2026 inda EFCC ke ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja da ta sallami Lamido da ’ya’yansa daga dukkan tuhume-tuhume a 2023.
Hukumar yaki da cin hanci ta nuna rashin jin daɗinta da hukuncin, inda a ranar 31 ga Yuli, 2023, ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli.
EFCC na neman Kotun Koli ta soke hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da mayar da shari’ar kotun farko domin ci gaba da sauraro.
A cewar EFCC, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi kuskure a doka wajen sallamar waɗanda ake zargi duk da hujjojin da suka nuna akwai shari’a a kansu.

Source: Facebook
Zargin da EFCC ke yi wa Lamido, ɗansa
EFCC ta zargi Lamido da wanke kuɗaɗen ₦1.35 biliyan, wanda ake cewa ya karɓa a matsayin rashawa daga ’yan kwangila.
Rahoton ya ce ’yan kwangilar sun aiwatar da ayyukan gwamnatin jihar Jigawa a lokacin da Lamido ke kan mulki.
Lamido ya shugabanci jihar Jigawa daga shekarar 2007 zuwa 2015 kafin shari’ar ta fara a shekarar 2015.
EFCC ta gabatar da shaidu sama da 16 kafin rufe ƙarar ta a kotu, sai dai maimakon fara kare kansu, waɗanda ake tuhuma sun gabatar da bukata da cewa babu laifi.
Mai shari’a Ojukwu ta ƙi amincewa da bukatar, tana mai cewa akwai shari’ar da za su amsa a kanta.
Wannan hukunci ne Lamido da sauran waɗanda ake tuhuma suka ɗaukaka ƙara, wanda hakan ya kai ga sallamarsu a Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Yanzu dai ana jiran hukuncin Kotun Koli domin yanke makomar shari’ar da ta shafe kusan shekaru 10 tana gudana.
'Zan iya barin PDP' - Sule Lamido
Kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa da yiwuwar ya tattara kayansa ya bar jam'iyyar PDP kafin zaben 2027.
Sule Lamido ya ce matukar abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, aka gaza samo mafita a rikicin PDP, babu shakka zai nemi jam'iyyar da ta dace da shi.
Ya nuna takaicinsa matuƙa kan abin da ya kira ƙoƙari da gangan da wasu mutane ke yi domin lalata tare da ruguza PDP gaba daya.
Asali: Legit.ng
