'Dabarar da Sojoji Ke Yi wurin Kubutar da Mutane daga Ƴan Bindiga': Ministan Tsaro
- Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya yi magana game da hare-haren yan ta'adda a fadin Najeriya gaba daya
- Musa ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane, duk da rade-radin jama’a
- Tsohon sojan ya bayyana dabarar da sojoji ke yi wajen tilasta ‘yan bindiga guduwa, su bar wadanda suka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja -.Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada matsayinta cewa ba ta biyan kudin fansa domin kubutar da mutanen da aka sace a fadin kasar.
Ta ce jami’an tsaro na dogaro ne da karfin soja da ayyukan leken asiri wajen ceto wadanda aka sace daga hannun ‘yan bindiga.

Source: Twitter
Ta'addanci: Gwamnatin tarayya ta haramta biyan kudin fansa
Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana haka a wata hira da BBC Hausa da wakilin Legit Hausa ya bibiya.
Ya ce duk da zaton jama’a cewa ana biyan kudin fansa, gwamnatin tarayya ba ta taba biyan ko sisin kwabo ga masu garkuwa.
Ya ce:
“Gwamnatin tarayya ba ta biyan kudin fansa. Ko da wasu na biya, mu ba ma biya kwata-kwata."
Musa ya bayyana cewa yawancin wadanda aka ceto suna samun ‘yanci ne bayan matsin lambar da jami’an tsaro ke yi wa ‘yan bindiga.
Ya ce idan aka sace dalibai daga makarantu, sojoji kan bi ‘yan bindiga cikin dazuka domin tilasta musu guduwa.
A cewarsa, a irin wannan yanayi ‘yan bindiga kan bar yaran, daga nan jami’an tsaro su dauko su cikin nasara.
Matsalar da biyan kudin fansa ke jawowa
Ministan ya jaddada cewa biyan kudin fansa na kara karfafa kungiyoyin ta’addanci tare da zaburar da karin sace-sace.
Ya bukaci iyalai da al’umma su rika kai rahoton sace-sace ga hukumomin tsaro maimakon shiga tattaunawa da masu laifi.
“Idan ana ci gaba da biyan fansa, hakan zai sa mutane su rika satar jama’a don neman kudi.
“Idan aka sace wani, abu mafi dacewa shi ne a sanar da jami’an tsaro domin daukar mataki na gaskiya.

Kara karanta wannan
"Abokin barawo": Ministan tsaro ya gargadi Sheikh Gumi da masu goyon bayan 'yan ta'adda
“Duk wanda ya sayar musu da abinci ya karbi kudi, to kudin jini yake ci, kuma wannan ba abu ne mai kyau ba."

Source: Facebook
Gargadin gwamnatin tarayya ga jihohi kan ta'addanci
Ya bukaci jama’a su ba da hadin kai, yana mai cewa bayanan sirri daga al’umma na da matukar muhimmanci wajen kawo karshen ‘yan bindiga.
Musa ya gargadi gwamnatocin jihohi da su guji shiga yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga.
Ya bayyana irin wadannan yarjejeniyoyi a matsayin yaudara da ke gurgunta kokarin tsaron kasa.
Ministan ya ambaci jihar Katsina a matsayin misali inda gwamnatin tarayya ta yi gargadi kan yin sulhu da kungiyoyi masu dauke da makamai.
A cewarsa, manufar gwamnatin tarayya a kowace rana ita ce tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin Najeriya.
Barazanar Turji na firgita al'ummar Sokoto
Mun ba ku labarin cewa shugabanni da masu ruwa da tsaki a garuruwan da ke gabashin jihar Sokoto sun yi ƙorafi kan barazanar hare-haren Bello Turji.
Mutanen suna neman agajin gaggawa daga gwamnati da jami’an tsaro domin kawo karshen ta'addanci da ya addabe su.
Mutanen fiye da ƙauyuka 20 sun tsere, yayin da wasu mazauna suka tsallaka zuwa Jamhuriyar Nijar domin tsira daga barazanar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
