Gwamnan Kaduna Ya Hango Abu Mai Kyau, Ya ba Yan Najeriya Mafita kan Dokar Haraji

Gwamnan Kaduna Ya Hango Abu Mai Kyau, Ya ba Yan Najeriya Mafita kan Dokar Haraji

  • Malam Uba Sani ya shawarci 'yan Najeriya da su rungumi dokokin haraji kuma su marawa gwamnatin tarayya baya wajen aiwatar da su
  • Gwamnan na jihar Kano ya ce gyaran da aka yi wa tsarin harajin zai taimaka wajen gina tubali mai karfi da zai kawo ci gaba a Najeriya
  • Ya kuma bukaci bangaren gwamnati da su rike amana, yana mai cewa ta haka ne mutane za su samu natsuwar biyan haraji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bukaci mutanen Arewa da sauran 'yan Najeriya da su ba da goyon baya ga sababbin dokokin haraji na kasa.

Sanata Uba Sani ya bayyana cewa dokokin haraji suna da muhimmanci kwarai wajen gina ginshikin ci gaba mai dorewa a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an gano dalilai 3 da suka jawo jinkirin sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC

Gwamnan Kaduna, Uba Sani.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani na jagorantar wani taro a fadar gwamnatinsa Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa Gwamna Uba Sani ya fadi haka ne yayin da yake jawabi a wurin wani taron wayar da kai da kungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya ranar Talata.

Uba Sani ya hango amfanin dokar haraji

Gwamna Uba, wanda shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Jihar Kaduna (KADIRS), Jerry Adams, ya wakilta, ya ce gyaran da aka yi wa tsarin harajin zai saukaka hanyoyin samun kudaden shiga na Najeriya.

A cewar gwamnan gyaran zai sa biyan haraji ya zama cikin sauki tare da samar da hanyoyin bunkasa kasuwanci, musamman ga sana'o'in da matasa ke jagoranta.

Haka zalika ya ce dokar harajin za ta hade hanyoyin tattara kudaden shiga daban-daban zuwa wuri guda, wanda zai rage rudani kuma ya kara saukin gudanar da kasuwanci.

Sakon gwamnan Kaduna ga matasan jihar

Gwamna Uba Sani ya bukaci matasa da su marawa wadannan sauye-sauyen haraji baya, yana mai jaddada cewa gudunmawarsu ita ce mabuɗin tabbatar da nasarar sababbin dokokin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta hango lam'a a kalaman Kwankwaso na tilasta wa masoyansa koma wa APC

"Dole mu ga gyaran haraji da aka yi yana haifar da sakamako na zahiri kamar kyawawan hanyoyi, ingantaccen ilimi, kiwon lafiya, ingantaccen tsaro, da fadada hanyoyin samun arziki,” in ji gwamnan.

Ya kara da cewa idan jama'a suka ga ana amfani da harajinsu wajen ayyukan ci gaba, hakan zai karfafa amincewar su ga gwamnati kuma ya karfafa gwiwar mutane su rika biyan haraji da kansu ba tare da an tursasa su ba.

Uba Sani da Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Gwamna Uba Sani a fadar shugaban kasa, Abuja Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

An aika sako ga gwamnonin Arewa

Da yake nasa jawabin, Muhammad Yakubu, shugaban kungiyar Arewa Think Tank, ya ce gyaran harajin wata dama ce ga jihohin Arewa su fito da sababbin dabarun kirkira, da dogaro da kai.

Yakubu ya bayyana cewa:

"Wadannan sauye-sauye za su karfafa kirkire-kirkire da kuma kara dankon zumunci tsakanin yak lasa da gwamnatin tarayya."

Ya yi kira ga shugabannin Arewa da su marawa tsarin baya, tare da shawartar jihohi su fito da hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu don kara kudaden shiga na cikin gida (IGR), kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Uba Sani ya ware wa kowace mazaba N100m

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya rattaba hannu kan dokar kasafin kudi ta shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sayo dankara dankaran motoci 65 na alfarma, ya rabawa sarakuna

Gwamna Uba Sani ya ware Naira miliyan 100 ga kowace mazaba cikin guda 255 da ake da su a jihar Kaduna cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Matakin da Gwamna Uba Sani ya dauka shi ne irinsa na farko a tarihin jihar, kuma ya yi daidai da kudurin gwamnan na bunkasa ci gaban al’umma daga tushe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262