"Abokin Barawo": Ministan Tsaro Ya Gargadi Sheikh Gumi da Masu Goyon bayan 'Yan Ta'adda

"Abokin Barawo": Ministan Tsaro Ya Gargadi Sheikh Gumi da Masu Goyon bayan 'Yan Ta'adda

  • Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya gargadi Sheikh Ahmed Gumi da duk masu nuna goyon baya ga ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji
  • Janar Christopher Musa ya bayyana cewa abokin barawo, barawo ne kuma ba za a sassauta wa duk wanda ya ke ci gaba da goyon bayan 'yan ta'adda ba
  • Ya bayyana cewa addini, kabila ko yanki ba shi da alaka da aikin ta'addanci da wasu ke da shi na ta'addanci da jawo asarar rayuka a sassan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya yi gargaɗi ga Sheikh Ahmed Gumi da sauran mutanen da ke nuna goyon baya ko tausayawa ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da makami.

Kara karanta wannan

Zafin siyasa bai hana aiki: Abba ya fadi shirin gwamnati a kan matasa 50, 000 a Kano

Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana cewa abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne, inda ya ce wajibi ne a daina duk wani yunƙuri na ɓoye-ɓoye ko mara wa masu aikata laifuffuka baya.

Christopher Musa ya ja kunnen masu ra'ayin Gumi a kan ta'addanci
Janar Christopher Musa mai ritaya, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi Hoto: Salisu Webmaster|Defence Headquaters
Source: Facebook

This Day ta wallafa cewa Janar Christopher Musa ya yi wannan bayani ne jiya yayin wata ziyarar aiki da ya kai Maiduguri, inda ya jaddada cewa ‘yan ta’adda da ‘yan fashi ba sa wakiltar wani yanki, addini ko kabila.

Janar Christopher Musa ya gargadi Ahmad Gumi

A wata hira da BBC Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook, Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana cewa duk wani yunƙuri na kare 'yan ta'adda ko nuna musu sassauci na ƙara jefa ƙasa cikin barazana.

Ministan tsaron ya bayyana cewa kalamansa ba na siyasa ba ne, illa magana ce ta kare rayuka da dukiyoyin talakawan Najeriya.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su guji ba da wani uzuri ko kariya ga aikata laifuffuka ta kowace hanya. Ya ce wannan gargadi martani ne ga wasu ra’ayoyi da Sheikh Gumi ya taɓa furtawa.

A kalaman da ya furta, Sheikh Gumi ya kira ‘yan fashin da ke buya a dazuka da suna ’yan uwanmu, tare da cewa al’umma ba za ta iya rayuwa ba tare da su ba.

Kara karanta wannan

Dabaru 2 da ministan Buhari, Lai Mohammed ya yi da suka jawo nasarar Tinubu a 2023

Kaunar 'yan ta'adda bai kawo karshen laifi - Janar Musa

A mataninsa, Janar Christopher Musa ya ce akwai bambanci a tsakanin tausayi da haɗin baki da laifi, yana mai cewa nuna jinƙai ga ‘yan ƙasa abu ne mai kyau, amma kare ko halatta ta’addanci yana ƙarfafa hanyoyin aikata laifi.

Ya ce waɗannan ƙungiyoyi sun lalata al’ummomi, sun kori dubunnan iyalai daga gidajensu, tare da hallaka rayukan bayin Allah marasa laifi a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Janar Christopher Musa ya ce ra'ayi irin na su Sheikh Gumi na da illa ga tsaron kasa
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi Hoto: Dr. Ahmad Mahmud Gumi
Source: Facebook

Janar Christopher Musa ya jaddada cewa kiran ‘yan fashi da suna ’yan uwa ba ya rage tashin hankali ko ya kawo zaman lafiya, sai dai yana halatta aikata laifi tare da raunana ƙoƙarin tsaro na ƙasa.

Tsohon hafsun sojan ya ce ce duk wanda ke kare wa, ya ke uzuri ko ke ɓoye masu laifi da bakinsa ko ta hanyar tsuke bakin, ya sani cewa yana da hannu a sakamakon ta'addanci a duniya.

Martanin Gumi ga Christopher Musa

A baya, mun wallafa cewa fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya sake bayyana matsayinsa kan matsalar rashin tsaro da ta addabi Najeriya.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Fitacciyar mawakiyar yabon addini ta riga mu gidan gaskiya

A cewarsa, sabanin ra’ayin da wasu ke dauka, ba ya kare ’yan ta’adda ko halatta abin da suke yi, illa kokarin isar da gaskiya da kuma sanar da su cewa ayyukansu haramun ne a addinin Musulunci.

Fitaccen malamin ya ce manufarsa ita ce nemo hanyoyin da za su kawo karshen zubar da jini da wahalhalun da fararen hula ke fuskanta, ba wai karfafa ta’addanci da ci jefa jama'a a musulunci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng