Bayan ba Sarakuna 65 Motoci, Gwamna Sheriff Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa

Bayan ba Sarakuna 65 Motoci, Gwamna Sheriff Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa

  • Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya yi sauye-sauye yayin da ya amince da garambawul a gwamnatinsa
  • Sheriff Oborevwori ya sauyawa wasu daga cikin kwamishinonin da ke gwamnatinsa ma'aikatun da za su jagoranta nan take
  • Hakazalika, Gwama Sheriff Oborevwori ya yi nade-nade a hukumar gudanarwar jami'ar jihar Delta da ke a garin Abraka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Delta - Yayin da aka shiga sabuwar shekara, Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi wani dan karamin garambawul a gwamnatinsa.

Gwamna Sheriff Oborevwori ya amince da yin sauye-sauye 'yan kaɗan a majalisar zartarwar jihar Delta.

Gwamna Oborevwori ya yi garambawul a gwamnatinsa
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori Hoto: Rt. Hon Sheriff Oborevwori
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Delta, Kingsley Eze Emu, ya sanya wa hannu, wadda aka raba wa manema labarai a birnin Warri ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

An ware kwanaki 4, za a birne mataimakin gwamnan da ya rasu a Najeriya

Gwamna Sheriff ya yi sauye-sauye

A cewar sanarwar, sauye-sauyen sun shafi kwamishinoni huɗu, inda Injiniya Michael Ifeanyi Anoka ya koma daga ma’aikatar tsare-tsare da sabunta birane zuwa ma’aikatar makamashi.

Sunday Tataobuzogwu ya bar ma’aikatar makamashi zuwa ma’aikatar tsare-tsare da sabunta birane, jaridar The Sun ta kawo labarin.

Haka kuma, an mayar da Misis Rose Ezewu daga ma’aikatar kula da harkokin ilimin sakandare zuwa ma’aikatar kula da harkokin ilimin firamare.

Hakazalika, sauyin ya shafi Kingsley Ashibuogwu, inda ya koma daga ma’aikatar kula da harkokin ilimin firamare zuwa ma’aikatar kula da harkokin ilimin sakandare.

Sanarwar ta tabbatar da cewa sauye-sauyen kwamishinonin za su fara aiki nan take duk da cewa ba ta bayyana dalilin da ya sa aka yi garambawul din ba.

An yi nade-naden mukamai a jihar Delta

A wani bangare na daban, Gwamna Oborevwori ya kuma amince da naɗin mutane uku cikin hukumar gudanarwa ta jami’ar jihar Delta da ke Abraka.

Kara karanta wannan

Shirin tsige Gwamna Fubara a Rivers ya sake gamuwa da cikas a majalisa

Mutanen da aka naɗa su ne Festus Ovie Agas, Frank Enekorogha da Charles Ajuyah (SAN). Dama can Festus Ovie Agas ya kasance tsohon sakataren gwamnatin jihar Delta.

Sanarwar ta kara da cewa za a sanar da ranar rantsar da mambobin kwamitin gudanarwar a nan gaba.

Gwamna Oborevwori ya sauyawa wasu kwamishinoni wurin aiki
Gwamna Sheriff Oborevwori na jawabi a wajen taro Hoto: Rt. Hon. Sheriff Oborevwori
Source: Facebook

Karanta wasu labaran kan jihar Delta

Gwamna Sheriff ya fice daga PDP zuwa APC

A wani labarin da muka taba kawo muku, kun ji cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Gwamna Sheriff Oborevwori ya bayyana sauya shekar a matsayin matakin da zai ƙarfafa haɗin gwiwar siyasa da tabbatar da ci gaban jihar Delta a matakin kasa.

Sauya shekar da gwamnan ya yi daga PDP na zuwa ne shekara biyu bayan ya lashe zabe karkashinta a shekarar 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng