Zafin Siyasa bai Hana Aiki: Abba Ya Fadi Shirin Gwamnati a kan Matasa 50, 000 a Kano
- Gwamnatin Kano ta shirya ƙara inganta rayuwar matasa, inda ta yi wa mutum 50,000 shiri na musamman a shekarar 2026
- Mai girma gwamna ya sanar da cewa an yi shirin ne musamman saboda imanin Gwamna Abba Kabir Yusuf a kan muhimmancin matasa
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa an tsara shirin ne domin samar da ƙwararrun matasa masu dogaro da kai a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Kano ta sanar da shirin horas da matasa aƙalla 50,000 a faɗin jihar nan a shekarar 2026, a wani yunƙuri na rage matsalar rashin aikin yi da kuma ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin matasa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin rabon kayayyakin tallafin ƙarfafa sana’o’i ga ɗalibai 2,260 da suka kammala karatu daga cibiyoyin koyon sana’o’i guda takwas a Jihar Kano.

Source: Twitter
Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a shafin Facebook cewa an yi bikin ne a Fadar Gwamnati da ke Kano, inda Gwamna ya nanata muhimmancin matasa ga ci gaban kasa.
Gwamnatin Abba za ta taimaki matasan jihar Kano
A cewar wata sanarwa d Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, shirin yana da nufin bai wa matasa ƙwarewar aiki domin su zama masu amfani ga tattalin arzikin jihar da kawunansu.
Gwamna Abba ya kara da cewa an tsara shirin ne domin samar da ƙwararrun matasa masu dogaro da kai, waɗanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kano.
Gwamnan ya ce:
“Manufarmu ita ce mu ba matasa ƙwarewa da damammakin da suke buƙata domin su tsaya da ƙafafunsu, su samu hanyar samun kuɗi, kuma su bayar da gudummawa mai ma’ana ga bunƙasar Jihar Kano.”
Ya ƙara da cewa shirin horaswar na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatinsa na yaki da talauci, rashin aikin yi, da tashin hankalin matasa a al’ummomi daban-daban na jihar.
Gwamna ya jinjina muhimmancin matasan Kano
A cewarsa, gwamnati na kallon matasa a matsayin muhimmin jigon samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen rayuwa da ƙarancin ayyukan yi.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari mai yawa a harkar ƙarfafa matasa, yana mai cewa wannan wata dabara ce ta tabbatar da ci al’umma a nan gaba.
Ya ce:
“Mun kuduri aniyar saka hannun jari a kan matasanmu, domin su ne kashin bayan ajandar ci gabanmu da kuma makomar wannan jiha.”
Gwamnan ya bayyana cewa shirin horaswar da ake shirin aiwatarwa zai ƙarfafa shirye-shiryen tallafi da gwamnatin jihar ke aiwatarwa a halin yanzu.
Ya ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da ɗaukar matakai masu ma’ana domin tabbatar da cewa matasa sun samu ƙwarewa, ayyukan yi, da damar da za su ba su gudummawa mai ɗorewa ga cigaban jihar.
Shugaba Bola Tinubu ya yabi mulkin Abba
A baya, mun wallafa cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, murnar zagayowar ranar haihuwarsa, tare da yabon jagorancinsa. Tinubu ya aika da saƙon taya murnar ne yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke cika shekaru 63 a duniya a ranar 5 ga Janairu, 2026, inda ya ce Gwamnan na bakin kokarinsa.
A cikin saƙon, shugaban ƙasar ya bayyana gwamnan a matsayin shugaba mai mutunci, karamci, sauƙin kai, kuma jajirtacce wajen gudanar da ayyukan gwamnati da taimakon talaka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


