Olubadan Ya Wanke Kansa daga Zargin Kunyata Mai Martaba Sarki a bainar Jama’a

Olubadan Ya Wanke Kansa daga Zargin Kunyata Mai Martaba Sarki a bainar Jama’a

  • Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, ya ce bai yi watsi da Alaafin na Oyo ba da gangan kamar yadda ake yadawa
  • Sarkin ya bayyana cewa tsarin ladabi a taro da lokacin shigarsa taron ne suka janyo abin da ya faru, ba raini ba
  • Olubadan ya jaddada muhimmancin haɗin kai da cigaban al’umma, yana kira da a daina karkatar da al’amura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.'B

Ibadan, Oyo - Olubadan na ƙasar Ibadan, Oba Rashidi Ladoja (Arusa I), ya yi karin haske kan rade-radin ya ki gaisawa da Alaafin na Oyo.

Sarkin ya karyata abin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya yi watsi da Alaafin na Oyo, Oba Akeem Owoade da gan-gan yayin wani taro a Ibadan, Jihar Oyo.

Olubadan ya magantu kan kin gaisawa da Alaafin na Oyo
Olubadan, Rashidi Ladoja da Alaafin na Oyo, Oba Akeem Owoade. Hoto: @Imranmuhdz.
Source: Twitter

Olubadan ya kare kansa daga sukar jama'a

Kara karanta wannan

Dabaru 2 da ministan Buhari ya yi da suka jawo nasarar Tinubu a 2023

Da yake magana da manema labarai a Ibadan, Olubadan ya ce halin da ya tsinci kansa a taron ne musamman ganin cewa ya isa wurin taron a ɗan makare, cewar Leadership.

Sarkin ya jaddada cewa abin da ya faru ba da gangan aka yi ba, kuma babu wata manufa ta raini ko rashin girmamawa, yana mai cewa lamarin kawai rashin fahimta ne da aka ƙara girmama shi fiye da kima.

Ya ƙara da cewa tsarin ladabi da tsari na zaman sarakuna ne ya tilasta masa ƙoƙarin zama a kujerarsa cikin natsuwa ba tare da katse taron ba.

Ya ce:

“Babu wata manufa ko kaɗan. Abin da ya faru ba da gangan aka yi ba. An fassara shi ta wata hanya daban, musamman a kafafen sada zumunta.
“Idan na makara zuwa wuri, ina ƙoƙarin shiga a hankali. Kamar yadda ake yi a masallaci idan salla ta kusa tsayawa. Ina so ne kawai in isa kujerata kafin a ce ba zan iya tafiya ba."
Olubadan ya fadi dalilin kin ba Sarki hannu a taro
Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja a taro lokacin da ya ki gaisawa da Alaafin na Oyo a taron addu'a Hoto: Arabinrin Opeyemi.
Source: Facebook

'Dalilin kin gaisawa da Alaafin' - Olubadan

Olubadan ya bayyana cewa kujerarsa tana tsakanin Soun na Ogbomosho da Alaafin na Oyo, lamarin da ya sa dole ya ratsa wasu ɓangarori na ɗakin taron.

Kara karanta wannan

Rigimar iko: Olubadan ya 'kunyata' Sarki mai martaba a tsakiyar taron jama'a a Najeriya

Sai dai lokacin da ya dawo, wasu daga cikin manyan baki sun riga sun matsa, wanda ya sa ya koma baya, cewar TheCable.

“Kujerata tana tsakanin Soun da Alaafin. Dole ne in ratsa wasu mutane kafin in isa. Ban yanke shawarar gujewa ko watsi da kowa ba. Me zai sa in yi haka?”

Sarkin ya nuna damuwa kan abin da ya kira yin sharri daga wasu masu sharhi, yana mai cewa bidiyon da aka yaɗa a intanet ba cikakken abin da ya faru ba ne.

“Idan an kalli cikakken bidiyon, za a ga ina gaisawa da mutane da dama, har da gwamna. Amma kafafen sada zumunta kan sauya abubuwa daga ma’anarsu."

- In ji Olubadan

Kwankwaso, Tinubu sun hadu a wurin nadin sarauta

A baya, kun ji cewa a ranar Juma'a, 26 ga watan Satumba, 2025 aka gudanar da bikin nadin sabon Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja a Oyo.

Manyan baki ciki har da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabi'u Kwankwaso sun halarci bikin.

Kwankwaso, wanda aka yi ta rade-radin zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, ya hadu da Bola Tinubu a wurin kuma sun gaisa cikin fara'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.