Fasto Kukah Ya Yi Amai Ya Lashe kan Zargin Kisan Kiristoci, Ya Tabo Musulmai
- Fasto Matthew Kukah ya yi martani game da rahotannin da ke cewa ya taɓa faɗin babu kisan Kiristoci a Najeriya
- Kukah ya ce an karkatar da kalamansa, yana jaddada cewa ana kashe Kiristoci kuma hakan bai kamata ya faru ba
- Limamin ya bayyana cewa matsalar tsaro na shafar duk ’yan Najeriya, Musulmi da Kiristoci ba tare da bambanci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fasto Matthew Kukah, na Cocin Katolika a Sokoto ya kuma yin magana game da zargin kisan Kiristoci a Najeriya.
Mathew Kukah ya musanta rahotannin da ke cewa ya taɓa faɗin cewa babu tsananta wa ko gallaza wa Kiristoci a Najeriya.

Source: Twitter
Kukah ya yi wannan bayani ne yayin da ya halarci wani shirin rediyo mai suna 'Boiling Point', wanda jaridar Punch ta bibiya.

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci
Donald Trump ya yi barazana ga Najeriya
A ranar 31 ga Oktobar 2025, Shugaban Amurka Donald Trump ya sake sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ake kira CPC sakamakon zarge-zargen cewa ana aiwatar da kisan kiyashi ga Kiristoci a ƙasar.
Kalmar CPC dai tana nufin ƙasa da ake zargi da take ’yancin addini da ke ci gaba da faruwa ba tare da katsewa ba. Gwamnatin Najeriya ta sha musanta zargin kisan kiyashi ga Kiristoci.
A ranar 25 ga Disambar 2025, Amurka ta kai hare-haren sama kan wasu sansanonin ’yan ta’adda biyu a dajin Bauni, da ke ƙaramar hukumar Tangaza a Jihar Sokoto.

Source: Twitter
Kukah ya musanta cewa ba a kashe Kiristoci
Yayin martanin, Kukah ya ce an karkatar da kalamansa game da zargin kisan kiyashi ko tsanantawa ga Kiristoci a ƙasar.
Sai dai ya ce ba a fahimci maganarsa ba kuma bai son komawa baya amma dai kowane addini ka ke za a iya sace ka a Najeriya, cewar TheCable.
Da yake magana kan cece-ku-cen, Kukah ya ce:
“Ban taɓa musanta cewa ana kashe mutanenmu (Kiristoci) ba. Abin da aka rika faɗa game da kalamaina ya ba ni mamaki sosai.
“Ko kisan kiyashi ko musgunawa wallahi wannan abu bai kamata ya faru ba. Duk inda za mu samu taimako, ko daga Trump ko wani, dole ne a hana waɗannan kashe-kashe.”
Kukah ya jaddada cewa matsalar rashin tsaro a Najeriya ba ta taɓa bambanta addini ba, yana mai cewa Musulmi da Kiristoci duk suna fuskantar barazanar sace-sace da hare-hare.
“Ko Musulmi ne, ko Kirista, kowa na cikin haɗarin sacewa a Najeriya."
- In ji Kukah
Fasto Kukah ya shawarci Tinubu kan tsaro
Kun ji cewa Fasto Mathew Kukah ya ce Najeriya ba za ta iya kawo ƙarshen ta'addanci da karfin soja kaɗai ba, domin bindiga ba ta kawar da akida.
Malamin cocin ya yi kira da a rungumi sulhu, shugabanci nagari, da adalci domin magance tushen rashin tsaro da tashe tashen hankula.
Ya gargadi Shugaba Bola Tinubu cewa ci gaban tsaro da ake gani a yanzu na wucin gadi ne, ba wai an kawo karshen matsalar kenan ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
