Jigon ADC Ya Zargi Tinubu da Sakaci, An Tsunduma Mutane Miliyan 141 a Bakin Talauci

Jigon ADC Ya Zargi Tinubu da Sakaci, An Tsunduma Mutane Miliyan 141 a Bakin Talauci

  • Daya daga cikin jagororin ADC mai adawa da gwamanti, Ladan Salihu, ya ce bakin talauci na ci gaba da samun gurbin zama a tsakanin 'yan Najeriya
  • Ladan Salihu ya jingina dalilansa na fadin haka da rahotannin Bankin Duniya da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), inda suka tabbatar da karuwar talauci a kasar
  • Babba a jam'iyyar adawar ya soki cire tallafin mai ba tare da isassun matakan rage radadi ba da sauran matakai da saka jama'a a cikin halin ni 'yasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jagora a jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC, Ladan Salihu, ya bayyana damuwa kan yadda talauci ke kara tsananta a Najeriya tun bayan shigowar gwamnati mai ci.

Ya bayyana cewa wannan ba kirkirarren labari ba ne, illa gaskiyar lamari kamar yadda bayanan Bankin Duniya da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) suka tabbatar.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu bayan Amurka ta kawo tallafin kayan aiki ga sojojin Najeriya

ADC ta zargi manufofin Tinubu da jefa jama'a a cikin wahala
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ladan Salihu ya yi wannan bayani ne a ranar Talata 13 fa watan Janairun shekarar 2026 yayin wata hira da kafar talabijin ta Arise.

Jagora ya koka kan karuwar talauci

Politics Nigeria ta ruwaito cewa inda Ladan Salihu ya ce kididdiga game da talauci a Najeriya ta kai kashi 43 cikin 100 a shekarar 2014, ta karu sosai zuwa 2019, sannan ta kara tabarbarewa zuwa 2025.

A cewarsa, wadannan alkaluma ba kirkirarru ba ne, yana mai jaddada cewa rahotannin Bankin Duniya da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ne suka wallafa su.

Ladan Salihu ya ce irin wadannan bayanai suna nuna matsalolin tsarin tattalin arziki da manufofin da ba su wadatar wajen kare rayuwar talakawa ba.

ADC ta ce an cire tallafin mai babu tallafin rayuwa
Alamar jam'iyyar ADC (h), Shugaba Bola Tinubu (d) Hoto: ADC Coalition 2027/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kuma soki gwamnatin jam’iyyar APC, yana cewa gyare-gyaren tattalin arziki da aka dauka sun yi tsauri fiye da kima, kuma hakan ya yi mummunar illa ga rayuwar jama’a da hanyoyin samun abin dogaro da kai.

Kara karanta wannan

Amurka ta kawo kayan aiki ga sojojin Najeriya kwanaki bayan farmakar 'yan ta'adda

Salihu ya bayyana cewa zuwa shekarar 2022, kusan ‘yan Najeriya miliyan 87 a Arewa da kuma miliyan 47 a Kudu ke rayuwa cikin tsananin talauci.

Wannan ya kai dadin mutanen masu rayuwa hannu baka, hannu kwarya zuwa miliyan 141 a fadin kasar. Ya ce wannan adadi ya kamata ya tayar da hankalin kowace gwamnati mai kishin jama’a.

Jagoran ADC ya zargi Tinubu da yin sake

Ladan Salihu ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da rashin gaskiya wajen fuskantar kalubalen tattalin arzikin kasar, yana mai cewa gwamnati ta dauki matakan da za su rage radadin talakawa, ba wai kara masu nauyi ba.

Salihu ya kara da cewa cire tallafin mai ba tare da isassun matakan rage radadi ba ya kara tsananta wahalhalun tattalin arziki.

Ya kwatanta halin da ake ciki da lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, inda ya ce an bullo da shirye-shirye da suka taimaka wajen rage matsalolin rayuwa ga ‘yan kasa.

Daga cikin irin wadannan shirye-shirye, ya ambaci Asusun Tallafawa Ilimi da Shirin Sufurin Jama’a wadanda a cewarsa sun taimaka wajen saukaka wa jama’a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ci gaba da ta'asa a Benue, an hallaka dan sanda da jikkata matafiya

Ya kuma yi nuni da tashin farashin sufuri bayan cire tallafin mai, yana cewa a shekarun 2014 da 2015, kudin tafiya daga Abuja zuwa Kano na kusan N1,500 ne, yayin da a yanzu ya kai 13,000 zuwa N15,000.

Jigon ADC ta fadi hanyar cire Tinubu

A baya, mun wallafa cewa wani babban jigo a jam’iyyar ADC, Dele Momodu, ya bayyana cewa jam’iyyarsu na cikin aikin sake fasali domin ta zama sahihin dandalin siyasa da ‘yan Najeriya za su iya dogaro da shi a zaben 2027.

Dele Momodu ya ce ADC na kokarin gyara kura-kuran da aka taba yi a baya tare da gina jam’iyya mai karfi da za ta iya kalubalantar jam’iyya mai mulki, har a kai ga samun nasarar doke Tinubu a babban zaben.

A cewarsa, ADC ta dukufa wajen gyara kundin tsarin mulkinta, tare da sake tsara tafiyar jam’iyyar domin ta dace da halin da Najeriya ke ciki a yanzu, wanda ya ba jama'a dama damar su zabe ta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng