Dubu Ta Cika: An Cafke Mutane 3 Dauke da Kayayyakin Hada Bama Bamai a Daura
- Rundunar 'yan sandan Katsina ta kama mutane uku dauke da na'urorin tayar da bama bamai sama da 10,000 a kan hanyar Daura
- An gano buhuna 30 na sinadarin gelatine, na hada bam masu nauyin kilo 2,200 yayin binciken sirri da yan sanda suka gudanar
- Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu inda 'yan sanda suka tabbatar da cewa zasu gurfanar dasu a kotu bayan kammala bincike nan kusa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Rundunar 'yan sandan Katsina ta sanar da nasarar kama wasu mutane uku da ake zargi da mallakar maƙudan sinadaran hada bam ba bisa ƙa'ida ba.
Wannan nasara ta zo ne sakamakon ƙarfafa sa ido da binciken sirri a kan manyan hanyoyin jihar kamar yadda Babban Sufeton 'yan sanda (IGP) Kayode Egbetokun ya bayar da umarni.

Source: Twitter
An cafke mutum 3 da kayan hada bam
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin rundunar na X, dauke da sa hannun mai magana da yawun 'yan sandan, Abubakar Sadiq.
Kakakin rundunar, ya bayyana cewa jami’an binciken sirri sun tare wata mota ƙirar Golf a ƙauyen Koza da ke ƙaramar hukumar Daura a ranar 7 ga watan Janairu, 2026.
Bayan gudanar da bincike na gaggawa a cikin motar da wani mai suna Jamilu Musa ke tuƙawa, an gano na'urar tayar da bama bamai guda 6,975 da aka ɓoye su a wani da hankali ba zai kai ba.
Bayan kama Jamilu, rundunar ta faɗaɗa bincikenta wanda ya kai ga cafke wasu mutane biyu, Ibrahim Murtala da Sulaiman Muhammad.
An cafke sinadaran hada bama-bamai
A yayin wannan bincike, rundunar 'yan sandan ta kuma yi nasarar gano wasu ƙarin abubuwan fashewa masu matuƙar haɗari da suka haɗa da:

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta fara binciken yadda likitoci suka bar almakashi a cikin wata mata
- Na'urar tayar da bama bamai na lantarki guda 7,500
- Buhuna 30 da rabi na sinadarin gelatine masu nauyin kilo 2,273.65.
Wanda ake zargi na farko, Jamilu, ya bayyana cewa ya karɓi waɗannan kayayyaki ne daga hannun wani mutum mai suna Najib, wanda yanzu haka ake nemansa, domin kai su garin Kwangolam da ke ƙaramar hukumar Mai’adua bayan ya ɗakko su daga jihar Kano.

Source: Twitter
Za a gurfanar da wadanda aka kama
Wannan kamun na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙaimi wajen hana 'yan ta'adda amfani da abubuwan fashewa (IEDs), in ji rahoton Channels TV.
Rundunar 'yan sandan jihar a ƙarƙashin jagorancin CP Bello Shehu ta jaddada cewa za ta ci gaba da yin amfani da dabarun binciken sirri don kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Katsina.
Abubakar Sadiq ya tabbatar da cewa za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike, yayin da ake ci gaba da farautar Najib da ya tsere.
NAFDAC ta kwace sinadaran hada bam
A wani labari, mun ruwaito cewa, NAFDAC ta gano sinadaran hada bam a gidan da ke Kwakwachi a Kano, inda aka kama lita 88,560 na sinadaran.
Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola, ta ce adadin sinadaran da aka kama zai iya tarwatsa gaba daya jihar Kano idan aka yi sakaci da su.
An kama manajan gidan, Sani Bala, yayin da ake ci gaba da neman ubangidansa da suka yi shekara biyu suna harkar ba tare da lasisi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

