Mutanen Kauyuka za Su Kaura domin Luguden Wuta kan 'Yan Bindiga a Dazuka

Mutanen Kauyuka za Su Kaura domin Luguden Wuta kan 'Yan Bindiga a Dazuka

  • Gwamnatin Jihar Neja ta ba mutanen da ke zaune a ƙauyukan da ke zagaye da yankin Tafkin Kainji wa’adin wata biyu domin barin yankin
  • Gwamna Mohammed Umaru Bago ya ce matakin ya zama dole domin bai wa jami’an tsaro damar kakkabe ’yan ta’adda da ke fakewa a dazuka
  • Masarautar Borgu da gwamnatin tarayya sun bayyana goyon bayansu ga shirin, tare da alkawarin haɗin gwiwa don dawo da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja – Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da ba mutanen da ke zaune a ƙauyuka a kusa da Tafkin Kainji wa’adin wata biyu domin ficewa daga yankin.

Gwamna Mohammed Umaru Bago ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya fadar Sarkin Borgu, Alhaji Muhammad Haliru Dantoro Kitoro IV, a New Bussa, sakamakon wani sabon harin ta’addanci da ya afku a yankin.

Kara karanta wannan

Sakon da Bello Turji ya aiko ya hargitsa mutane, an fara guduwa a jihar Sakkwato

Gwamna Umaru Bago a fadar Borgu
Gwamnan Neja, Umaru Bago na magana a fadar Sarkin Borgu. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Balogi Ibrahim ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya ce matakin na daga cikin sabon salo da gwamnatinsa ke dauka, tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya, domin magance matsalar tsaro a yankunan da ke zagaye da Tafkin Kainji.

Kauyuka za su kaura a Neja

Gwamna Bago ya bayyana cewa sauya wa mutanen matsuguni ya zama dole ne domin hana su shiga matsala yayin da jami’an tsaro ke shirin luguden wuta a dazukan yankin.

Rahotanni sun nuna cewa ya ce bayanai sun nuna cewa ’yan bindiga da masu aikata laifuffuka suna fakewa yankin Tafkin Kainji a halin yanzu.

Ya kara da cewa gwamnati na da niyyar kakkabe dukkan masu aikata laifi daga dazukan, tare da mayar da yankin wuri mai aminci da al’umma za su zauna lafiya.

Gwamnan ya kuma nuna damuwa kan yadda mutane ke shigowa masarautar ba tare da tantance su ba, yana mai cewa hakan ya zama babbar barazana ga tsaro da kuma taimakawa ayyukan masu ba da bayanan sirri ga ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Kiran hadin gwiwa da masarautar Borgu

Gwamna Bago ya bukaci Majalisar Masarautar Borgu da ta tashi tsaye wajen sauke nauyinta, ta hanyar hada kai da hukumomin tsaro da kuma gwamnati a dukkan matakai.

Ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga Sarkin Borgu da daukacin al’ummar masarautar, musamman iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin, yana mai addu’ar samun rahamar Allah ga wadanda suka rasu da juriya ga iyalansu.

Karamin ministan noma da tsaron abinci, Dr Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce gwamnatin tarayya za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin kasa.

Jami'an tsaro a fadar Borgu
Sojoji da 'yan sanda a fadar Sarkin Borgu. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

A nasa bangaren, Sarkin Borgu, Alhaji Muhammad Haliru Dantoro Kitoro IV, ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da hukumomin da abin ya shafa domin gano da hukunta masu ba da bayanan sirri ga ’yan ta’adda.

An ce harin Amurka ya kashe Lakurawa

A wani labarin, kun ji cewa wata cibiya ta fitar da rahoto game da harin da sojojin Amurka suka kawo jihar Sokoto a Arewa ta Yamma.

Kara karanta wannan

Halin da aka shiga bayan farmakar Hausawa a jihar Edo

Rahoton da cibiyar ta fitar ya yi ikirarin cewa harin ya jawo kashe 'yan ta'addan Lakurawa sama da 150, yayin da da dama suka jikkata.

A wani bangare kuma, wani bincike da aka yi ya ce farmakin bai kai ga kan 'yan ta'addan ba, lamarin da ya jefa shakku kan ikirarin cibiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng