Majalisa Za Ta Haramta Zina, Ta Ƙaƙaba Hukunci Mai Tsanani? Gaskiya ta Fito
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Ƴan majalisar dokokin Akwa Ibom sun yi magana kan jita-jitar za su kawo kudirin haramta zinace-zinace a jihar
- Majalisar ta yi gaggawar karyata rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tana duba kudirin dokar domin amfani da ita
- Rahoton ya yi ikirarin cewa an tanadi hukunci ga mata marasa aure, yayin da mazan aure za su biya tarar miliyoyi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom ta musanta rahotannin da ke yawo a intanet game da haramta zina.
Majalisar tarayya ta ƙaryata cewa ‘yan majalisar na nazarin kudirin dokar haramta zina a tsakanin al'ummar jihar.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata 13 ga watan Janairun 2026, Jerry Anson Otu, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, ya ce ikirarin karya ne kuma ba shi da tushe, cewar TheCable.

Kara karanta wannan
An dakatar da likitoci kan barin almakashi a cikin matar aure yayin tiyata a Kano
An yada cewa za a haramta zina a Akwa Ibom
Wasu rahotanni musamman a kafafen sada zumunta sun ce kudirin dokar na da alaka da mataimakiyar gwamna, Sanata Akon Eyakenyi.
Rahoton ya yi ikirarin cewa kudirin dokar zai hukunta mata marasa aure da daurin shekaru 10 idan aka same su da zina da mazan aure.
Ya kuma ce mazan auren da ke aikata irin wannan laifi za su biya tarar Naira miliyan biyu kacal ba tare da dauri ba.

Source: Original
Martanin majalisa kan kudirin haramta zina
Sai dai majalisar karkashin shugabanta, Udeme Utong ba ta yi magana ko duba irin wannan kudiri ba, yana kira ga jama’a su yi watsi da labarin bogi da ke yunkurin bata suna.
Majalisar ta ƙaryata rahoton da ake yadawa inda ta ce babu wannan magana kuma ko shawarar haka ba a bayar ba, cewar Premium Times.
Sanarwar ta ce rahoton, wanda aka yada, ya yi ikirarin cewa kudirin zai hukunta mata daurin shekaru 10 a gidan yari idan aka same su da yin hulɗar jima’i da mazan aure, yayin da maza za su fuskanci tarar ₦2m.
Sanarwar ta ce:
“Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom na son bayyana a sarari cewa wannan rahoto ƙarya ce tsagwaron gaske kuma babu wata hujja a kansa.
"Majalisar ba ta karɓa ko tattauna irin wannan kudiri ba, kuma mataimakiyar gwamnan ba ta dauki nauyinsa ba.
“Mu na Allah wadai da wannan mugun yunkuri na ɓata sunan mataimakiyar gwamna da Majalisar, kuma muna kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labarin ƙarya da duk wani sharhi da ke da nasaba da shi.
“Majalisar na ci gaba da jajircewa kan rawar da kundin tsarin mulki ya dora mata na kafa dokoki, kuma ba za ta bari wasu miyagu su tauye mutuncinta ba.”
Gwamna ya yi alkawarin ba makaho albashin N1m
A baya, mun ba ku labarin cewa Gwamna Umo Eno ya tallafa wa mawakin makaho fili, gida, da jarin miliyoyi domin karfafa dogaro da kai a Akwa Ibom.
Gwamnan ya ce za su gina masa gida mai ɗakuna huɗu, su samar masa da shagon aiki, tare da ba shi alawus duk wata.
Eno ya jaddada cewa Chris Vic ya zama abin koyi ga masu nakasa, yana nuna yabon Allah yana yiwuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
