Tirkashi: Mutane sun fito kwansu da kwarkwatarsu suna zanga-zanga saboda gwamnati za ta sanya dokar hana zina

Tirkashi: Mutane sun fito kwansu da kwarkwatarsu suna zanga-zanga saboda gwamnati za ta sanya dokar hana zina

- Mutane sun fito kwansu da kwarkwatarsu a birnin Jakarta na kasar Indunusiya inda suke zanga-zanga akan wata doka da gwamnatin kasar za ta sanya

- A ranar Talatar nan ne da ta gabata majalisar kasar ta fito da wata sabuwar doka da za ta haramta yin zina kwata-kwata a kasar

- Inda ta bayyana cewa za ta daure duk wani mutumi da aka kama ya kwanta da mace ba tare da aure tsakaninsu ba

'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa da ruwa akan wasu masu zanga-zanga a lokacin da suka yi cincirindo a gaban dakin majalisar kasar Indunusiya, akan sabuwar dokar da ake shirin sanyawa da za ta hana yin zina da mace kafin aure.

Wannan zanga-zanga akan wannan doka dai an yita a sauran birane dake fadin kasar. Dokar a cewar BBC za ta rage yawan zubar da ciki, yanzu haka dai ba a sanya hannu akan dokar ba, amma dai masu zanga-zangar suna ganin cewa dole 'yan majalisar za su sanya hannu akan dokar.

Dokar dai da majalisar kasar za ta sanya, za ta sanya hukuncin shekara daya a gidan yari ga duk wanda aka kama yana zina da mace ba tare da aure ba, sannan kuma wadanda aka kama su sunyi suna da aure za a yanke musu hukuncin wata shida a gidan yari.

Haka kuma duk wanda aka kama da laifin zubar da ciki za a yanke musu hukuncin shekara hudu a gidan yari, idan har zubar da cikin ba yana da nasaba da rashin lafiya ko fyade ba.

KU KARANTA: Innalillahi: Ana kashe Musulmi ana cire sassan jikinsu a sanyawa 'yan wasu addinin a kasar China

Ana mika wannan sabuwar doka ne dai ranar Talatar nan da ta gabata, sai dai kuma shugaban kasar Joko Widodo ya daga yin kuri'a akan wannan dokar har zuwa gobe Juma'a inda yace suna bukatar yin tunani mai zurfi akan wannan sabuwar doka.

Duk da jinkirin da aka samu wajen sanya hannu akan dokar, amma masu zanga-zangar suna ganin cewa a kowanne lokaci za a iya sanya hannu akan dokar.

Wannan zanga-zanga dai tafi karfi a babban birnin kasar na Jakarta a yayin da masu zanga-zangar suka bukaci ganin Kakakin majalisar kasar Bambang Soesatyo. Sun yi ta jifan 'yan sanda da duwatsu, inda su kuma 'yan sandan suka yi ta jefa musu barkonon tsohuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel