Gbajabiamila Ya Tabo Batun Auren Hadiza Bala Usman, Ta Shiga daga ciki a Asirce
- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yabawa Hajiya Hadiza Bala Usman kan rawar da take takawa a gwamnatin tarayya
- Gbajabiamila ya yi wannan jawabi ne a babban taron murnar cikar Hadiza Bala Usman shekara 50 da haihuwa, har ya tabo batun aurenta
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati su dage kan gaskiya da sadaukarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya yi jawabi mai cike da yabo da girmamawa ga Hajiya Hadiza Bala Usman.
Hajiya Hadiza Bala Usman, ita ce mai ba Shugaban kasa shawara ta musamman kan daidaita manufofi da ayyukan gwamnati.

Source: Twitter
The Guardian ta wallafa cewa Gbajabiamila ya yi wannan jawabi ne a babban taron murnar cikar Hadiza Bala Usman shekara 50 da haihuwa, inda manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane suka halarta.

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci
Femi Gbajabiamila ya yabi Hadiza Bala Usman
A cewarsa, irin aikin da Hadiza Usman ke yi na sa tana hulda kafada da kafada da ofishin Shugaban Ma’aikata, lamarin da ke ba ta damar ƙara karfafa manufofin gwamnatin tarayya.
Ya ce Hadiza Bala Usman ta kasance mutumiyar da ke sauƙaƙa aiki, yana mai cewa gudunmawar da take bayarwa ta taimaka matuƙa wajen ciyar da harkokin gwamnati gaba.
Gbajabiamila ya bayyana jin daɗinsa da yadda take ƙara wa ofishinsa da ma gwamnati gaba ɗaya kima da inganci.
A kalamansa:
“Ina matuƙar godiya da irin ƙimar da ki ka ƙara wa ofishina da wannan gwamnati,” in ji Gbajabiamila.
“A madadin dukkan mutanen da ke nan da waɗanda ba su samu halarta ba, amma rayuwarsu na samun tasiri ta hanyarki, ina yi miki fatan cikar shekaru 50 cikin farin ciki.”
Ya kuma yi mata addu’ar samun ƙarin shekaru masu cike da kwanciyar hankali, lafiya, wadata da kuma albarkar Allah Mai jinƙai.
Gbajabiamila ya zolayi Hadiza Bala-Usman
A wani bangare na jawabin nasa, Gbajabiamila ya yi barkwanci kan aurenta na baya-bayan nan, inda ya ce duk da kusancin da ke tsakaninsu, Hadiza Usman ba ta sanar da shi batun auren ba.
Ya bayyana yadda ta ziyarce shi a gidansa ranar Kirsimeti a Legas, suka ci abinci tare, suka taya juna murna, amma ba ta ambaci komai game da aure ba.

Source: Twitter
Ya ce har yanzu tana ta neman yafiyarsa, sai ya ce cikin raha:
"Na yafe miki, Hadiza. Ina yi miki fatan zaman aure cikin farin ciki da kwanciyar hankali.”
Shi ma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi jawabi a taron, inda ya ja hankalin ma’aikatan gwamnati da su kasance masu sadaukarwa da ladabi a wajen aiki.
Kashim Shettima ya bayyana Hadiza Bala Usman a matsayin abin koyi ba ga ‘yar Arewa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
A cewarsa, tarihinta a aikin gwamnati ya ginu ne a hankali ta hanyar ɗaukar nauyin aiki, jajircewa da ƙarfafa cibiyoyi.
Hadiza Usman ta caccaki tsohon minista
A baya, mun wallafa cewa hadimar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Hajiya Hadiza Bala Usman, ta soki tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, kan zargin da ya yi mata dangane da littafin da ta wallafa.
A kwanakin baya, Mista Rotimi Amaechi ya bayyana cewa abin da Hadiza ta rubuta a littafinta game da shi ƙarya ce tsagwaronta, lamarin da ya sa ta yi gaggawar mayar masa da martani kan kalamanta.
Hadiza Usman ta fito, inda ta bayyana cewa tsohon ministan ya daina ƙaryata gaskiya, tana mai jaddada cewa abin da ta rubuta ya samo asali ne daga abubuwan da ta fuskanta kai tsaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

