Neman Sulhu: Ƴan Bindiga Sun Gindaya wa Gwamnatin Katsina Sharudda 8 Masu Tsauri

Neman Sulhu: Ƴan Bindiga Sun Gindaya wa Gwamnatin Katsina Sharudda 8 Masu Tsauri

  • 'Yan bindiga sun kashe mutane a hari da suka kai Kankara yayin da gwamnatin Katsina ke shirin sakin 'yan ta'adda 70 da aka kama
  • Kwamishinan tsaro Nasir Muazu ya bayyana cewa sakin yan bindigar na daya daga cikin sharudda takwas na yarjejeniyar sulhu
  • Mazauna yankin sun bayyana fargabar cewa yan bindiga na sake kai hare-hare duk da yarjejeniyar sulhun da aka kulla

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Duk da ƙoƙarin sulhu da gwamnatin Katsina ke yi, an samu wani sabon harin ta’addanci a yankin Kankara, inda ’yan bindiga suka farmaki amarya da wasu 'yan biki a ƙauyen Unguwar Nagunda.

Wannan hari da ya faru a daren Lahadi, 11 ga Janairu, 2025, ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane biyu, lamarin da ya jefa al'ummar yankin cikin fargaba da tunanin ko yarjejeniyar zaman lafiya ta wargaje.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi wa 'yan bindiga raga raga yayin artabu a Kaduna

'Yan bindiga na kai hare-hare a Katsina duk da yarjejeniyar sulhu
Jagoran 'yan bindiga, Ado Aliero yana jawabi a taron sulhu a Faskari, da Gwamnan Katsina, Dikko Radda. Hoto: @DanKatsina50, @dikko_radda
Source: Twitter

Gwamnati ta amince da yarjejeniyar sulhu

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Katsina, ta bakin kwamishinan tsaro, Nasir Muazu, ta bayyana shirinta na sakin wasu 'yan bindiga 70, in ji rahoton Daily Trust.

Gwamnatin ta ce wannan matakin wani muhimmin sharaɗi ne na yarjejeniyar zaman lafiya da al’ummomin yankin suka ƙulla da ’yan ta’adda.

A cewar kwamishinan tsaron, cika sharudan yarjejeniyar sulhun zai samar da sauƙin hare-hare da kuma ceto rayukan mutanen da ke tsare a hannun maharan.

'Yan bindiga sun gindaya sharudda 9

Kwamishina Nasir Muazu, a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, ya bayyana cewa yarjejeniyar ta dogara ne kan wasu tsauraran sharaɗoɗi da bangarorin biyu suka amince wa juna.

Waɗannan sharaɗoɗin sun haɗa da:

  1. Bada damar ’yan bindiga su shiga kasuwanni don saye da sayarwa.
  2. Kyale 'yan bindiga su ziyarci asibitoci ba tare da tsangwama ba.
  3. Bada dama ga ’yan bindiga su ziyarci danginsu
  4. Ba 'yan bindiga damar cudanya da jama'a ba tare da tsoron kama su ba.
  5. ’Yan bindigar sun amince za su daina kai hare-hare garuruwa.
  6. Za su daina yin garkuwa da mutane
  7. Sannan za su saki dukkan waɗanda suke tsare da su.
  8. Gwamnatin Katsina kuma za ta saki 'yan bindigar da aka kama, bayan an tantance su a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina za ta fito da ƴan bindiga 70 daga gidan yari, ta kafa hujjoji

Muazu ya jaddada cewa ko da yake gwamnati ba ita ta fara tattaunawa kai-tsaye da maharan ba, amma tana goyon bayan matakin al’umma domin an riga an samu nasarar sakin mutane kusan 1,000 sakamakon wannan yarjejeniya.

Mazauna wasu yankunan Katsina sun koka kan hare-haren 'yan bindiga duk da yarjejeniyar sulhu.
Taswirar jihar Katsina, inda 'yan bindiga suka gindaya sharuddan zaman lafiya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Fargabar mazauna jihar Katsina

Duk da waɗannan bayanan na gwamnati, mazauna yankin Kankara sun bayyana damuwa kan yadda ’yan bindiga ke sake kai masu hare hare.

Wasu mazauna yankin na ganin cewa maharan da suka kai harin Unguwar Nagunda na daga cikin rukunin da ke adawa da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanya wa hannu kwanan nan a ƙauyen Kakumi na ƙaramar hukumar Bakori.

Al’ummar yankin sun yi kira ga hukumomi da su ƙara tura jami’an tsaro, domin zaman lafiyar da ake magana a kai har yanzu akwai shakku a cikinsa yayin da jini ke ci gaba da zuba.

Za a saki 'yan bindiga 70 a Katsina

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, Gwamnatin Katsina ta ce sakin wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci mataki ne na tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar.

Kwamishinan tsaro Nasir Muazu ya kwatanta matakin da musayar fursunonin yaki inda ya ce an riga an saki mutane 1,000 da aka sace a baya.

Yunkurin gwamnati na sakin 'yan bindigar 70 ya gamu da gagarumar suka daga 'yan kasa, sai dai, gwamnatin Katsina ta kare kanta da hujjoji masu karfi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com