Za a Goyi Bayan Kasashen Duniya Su Sa Ido don Hana Magudi a Zaben 2027

Za a Goyi Bayan Kasashen Duniya Su Sa Ido don Hana Magudi a Zaben 2027

  • Tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce zai yi maraba da saka idon ƙasashen duniya idan hakan zai tabbatar da sahihancin zaɓen 2027
  • Tambuwal ya danganta matsayarsa da abin da ya faru a zaɓen 2015, inda hulɗar ƙasashen waje ta taimaka wajen samar da inganci a zaben da aka yi
  • Baya ga haka, Tambuwal ya ce ba tsoma baki kai tsaye yake nufi ba, yana nufin samar da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu bin tsarin dimokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya ce zai goyi bayan saka idon ƙasashen duniya a zaɓen 2027, muddin hakan zai taimaka wajen tabbatar da sahihancinsa.

Ya ce tarihin siyasar Najeriya ya nuna cewa hulɗar ƙasashen waje na iya taka rawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, musamman idan aka yi ta cikin tsari da mutunta ikon ƙasa.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Ana neman Tinubu ya dawo da Nasir El Rufa'i cikin jam'iyyar APC

Aminu Waziri Tambuwal
Sanata Aminu Waziri Tambuwal yana wani jawabi. Hoto: @AWTambuwal
Source: Twitter

Tambuwal ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi a tashar Arise TV, inda ya bayyana matsayarsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin haɗakar ’yan adawa da ke samun goyon bayan jam’iyyar ADC.

Maganar duba zaben Najeriya daga waje

A cewar Tambuwal, sa-hannun ƙasashen duniya a zaɓen 2015 ya taimaka wajen samar da yanayin da ya kai ga nasarar jam’iyyar APC a kan gwamnatin da ke kan mulki a wancan lokaci.

Ya bayyana cewa shi kansa ya kasance mamba a APC a lokacin zaɓen, lamarin da ya sa ya shaida tasirin da hulɗar ƙasashen duniya ta yi wajen ƙarfafa sahihancin tsarin zaɓen.

Tambuwal ya ce ba wai yana neman wata ƙasa ta zo ta tsoma baki kai tsaye ba ne, yana nufin a samu haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu bin tafarkin dimokuraɗiyya domin tabbatar da adalci da gaskiya.

Korafi game da zaben Najeriya

Kara karanta wannan

'Harin sojojin Amurka a Najeriya ya kashe Lakurawa 155,' Rahoto

Sanatan ya jaddada cewa duk da muhimmancin hulɗar ƙasashen waje, ba ita kaɗai ce hanyar da za a tabbatar da sahihin zaɓe ba.

A cewarsa, akwai buƙatar gyare-gyare a cikin gida, haɗa kai tsakanin masu ruwa da tsaki, da kuma bin doka da ƙa’idoji domin cimma burin zaɓe mai inganci.

Mutane a layin zabe a Najeriya
Mutane a layi yayin zabe gwamna a Anambra a 2025. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Ya ce sa-hannun ƙasashen duniya na daga cikin hanyoyi da dama da za su iya taimakawa wajen matsa lamba ga masu iko su yi abin da ya dace.

Daily Trust ta rahoto cewa baya ga maganar zaɓe, Tambuwal ya tabo batun tsaro, inda ya yi tsokaci kan rahotannin sa-hannun sojojin Amurka a Najeriya a watan Disamban 2025.

Ya bayyana fatan cewa irin wannan lamari ba zai sake faruwa ba, sai dai a samar da cikakken tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin biyu.

Ana so Tinubu ya dawo da El-Rufa'i

A wani labarin, kun ji cewa an fara kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya fara shiri na gaske domin tunkarar babban zaben shekarar 2027.

Wani jigo a APC, Salihu Isa Nataro ya bukaci shugaba Tinubu ya maido tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i cikin jam'iyyar APC.

Nataro ya kara da cewa dawo da El-Rufa'i APC zai taimaka wajen karfafa jam'iyyar tare da tabbatar da nasarar shugaba Tinubu a Arewa ta Yamma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng