Gwamnatin Kano Ta Fara Binciken Yadda Likitoci Suka Bar Almakashi a Cikin Wata Mata
- Hukumar kula da asibitocin Kano ta fara bincike kan mutuwar wata baiwar Allah, Aishatu Umar a cibiyar Abubakar Imam 'Urology Centre' da ke jihar
- Sanarawar da jami'ar hulda da jama'a ta hukumar, Samira Suleiman ta fitar ta ce an fara binciken ne sakamakon zargin sakaci da dangin marigayiyar suka yi
- Hukumar ta ce za a gudanar da bincike cikin gaskiya da ƙwarewa ba tare da son kai ba domin gano gaskiyar barin almakashi a cikin Aishatu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar kula da manyan asibitoci ta jihar Kano ta fara bincike kan zargin sakaci da ake yi bayan rasuwar wata mara lafiya mai suna Aishatu Umar a Cibiyar Abubakar Imam 'Urology Centre.'
An dauki wannan mataki ne sakamakon ƙorafe-ƙorafen jama’a da kuma zargin da iyalan marigayiyar suka yi cewa yanayinta ya tabarbare ne yayin da take karɓar kulawa a cibiyar.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun ci gaba da ta'asa a Benue, an hallaka dan sanda da jikkata matafiya

Source: Facebook
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Samira Suleiman kuma ta wallafa a shafinta na Facebook.
Kano: An fara binciken mutuwar Aisha
Sanarwar ta bayyana cewa Dr. Mansur Mudi Nagoda ya ji koken iyalan Aishatu Umar, wanda ya nemi a gaggauta bude bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Iyalan marigayiyar sun yi zargin cewa rashin kulawa yadda ya kamata ya taimaka wajen tsananta halin da marigayiyar ke ciki har ta rasa ranta.

Source: Original
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talata, ta ce ta lura da rahotannin da ke bayyana yadda lamarin ya faru, inda aka bayyana shi a matsayin abin tayar da hankali da damuwa ga jama’a.
Hukumar Kula da Asibitocin ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiyar, tare da jaddada cewa za ta dauki lamarin da matuƙar muhimmanci.
Sanarwar ta nuna cewa hukumar ba za ta yi sakaci ba wajen gano gaskiyar abin da ya faru, domin kare mutuncin aikin lafiya rayukan jama'a.
Hukumar asibittocin Kano ta dauki alkawari
A cewar sanarwar da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Samira Suleiman, ta sanya wa hannu, Dr. Nagoda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike nan take kuma na tsakani da Allah.
Suleiman ta tabbatar da cewa binciken zai shafi dukkannin matakan likitanci da na gudanarwa da suka shafi kulawar da aka bai wa marigayiyar tun daga shigarta cibiyar har zuwa lokacin rasuwarta.
A cikin sanarwar, an ambato Dr. Nagoda yana cewa:
“Binciken zai kasance a bayyane, ba tare da son kai ba, kuma za a yi shi a cikin kwarewa.”
Ya kara da cewa duk wani mataki da ya dace za a dauke shi bisa ka’idojin da aka tanada idan aka tabbatar da sakaci daga wani bangare.
Baiwar Allah ta rasu a asibitin Kano
A wani labarin, kun ji cewa wata mata mai juna biyu mai suna Shema’u Sani Labaran ta rasa ranta a Asibitin Kwararru na Abdullahi Wase da ke Kano, bayan da aka ce an samu jinkiri wajen ba ta kulawar gaggawa.

Kara karanta wannan
An cafke jami’in DSS da ake zargi ya tursasa wa budurwa barin Musulunci bayan dirka mata ciki
Rahotanni sun bayyana cewa matsalar ta shafi jinkirin shigar kudi zuwa asusun asbiti, sannan ana zarginsu da halin ko-in-kula daga bangaren wasu ma’aikatan asibitin har ya jawo rasuwarta.
Mijin marigayiyar, Mallam Bello Fancy, ya ce sun kai matarsa asibiti ne a lokacin da ta fara nakuda, amma aka ki karɓarta saboda ya zo da tsofaffin kudi, kuma asibitin ba shi da na’urar POS.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
