"Ba Mu Yadda da Su ba": Amotekun Ta Tare Mota Ɗauke da Hausawa a Hanyar Ondo

"Ba Mu Yadda da Su ba": Amotekun Ta Tare Mota Ɗauke da Hausawa a Hanyar Ondo

  • Rundunar tsaron Amotekun ta jihar Ondo ta tare wata mota dauke da mutane 38 da ake zargin sun fito daga Arewacin Najeriya
  • An kama su ne a Akure yayin sintirin tsaro, inda jami'an Amotekun suka ce an yi haka ne saboda akwai alamar tambaya a tare da su
  • Hukumar ta ce ana ci gaba da bincike da tantance bayanan kowa da kowa daga cikin mutane 38 din da aka kama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ondo – Rundunar tsaron jihar Ondo, wato Amotekun, ta tare wata babbar mota makare da gawayi da ke dauke da mutane 38 ‘yan Arewa a hanyarsu ta shiga Akure, babban birnin jihar.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi yayin wani aikin sintiri na yau da kullum a yankin Cathedral da ke cikin birnin Akure, a karamar hukumar Akure ta Kudu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki amarya da wasu 'yan gidan biki, an rasa rayukan bayin Allah

Amotekun sun kama Hausawa a Ondo
Wasu daga cikin dakarun Amotekun Hoto: Amotekun Corps
Source: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito jami’an Amotekun sun dakatar da motar ne bayan sun lura da wasu abubuwa da suka janyo shakku a kan mutanen.

Amotekun ta cafke Hausawa a jihar Ondo

RFI ta wallafa cewa an bayyana cewa mutanen suna tafiya ne a cikin sabuwar motar Mercedes-Benz, mai lambar rajista GML 335 XR, Jigawa.

Sai dai bayan tsayawa, fasinjojin ba su iya yin cikakken bayani kan dalilin shigarsu jihar Ondo ko inda suka nufa a cikin garin ba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, Kwamandan rundunar Amotekun, Cif Adetunji Adeleye, ya ce bayan jerin tambayoyi da aka yi masu, mutanen sun kasa bayyana manufarsu a Ondo.

A cewarsa, a halin yanzu ana ci gaba da tantance bayanan kowane mutum domin gano hakikanin asalinsu da niyyarsu da shiga jihar da yawansu.

Ya jaddada cewa duk wanda bincike ya nuna yana da laifi, za a hukunta shi bisa doka, yayin da wadanda aka wanke za a mayar da su jihohin da suka fito.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: An jibge jami'an tsaro, motocin yaki a kofar gidan gwamnatin Kano

Ana binciken Hausawa da Amotekun ta kama

Kwamandan Amotekun ya kara da cewa wurin da direban motar ya ce an dauki fasinjojin na daga cikin wuraren da ake dauka a matsayin tashar barazanar tsaro, abin da ya kara tsananta shakku kan matafiya.

Majiyoyi sun bayyana cewa yawancin fasinjojin matasa ne masu shekaru tsakanin 20 zuwa 27. Sun shaida wa jami’an tsaro cewa suna tafiya Ondo ne domin ziyartar ‘yan uwansu.

Amotekun ta ce an kama Hausawan saboda gaza gamsar da jami'ai
Taswirar jihar Ondo, inda aka kama Hausawa sama da 30 Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wata majiya ta ce shakku ya kara karfi ne bayan an samu daya daga cikin mutanen dauke da wata rigar aiki mai rubutun “Commander”, tare da wasu kayan al’ajabi.

A gefe guda kuma, direban motar da mai taimaka masa sun shaida wa jami’an Amotekun cewa sun dauki fasinjojin ne a hanya, ba su da wata alaka ta baya da su.

A halin yanzu, bincike na ci gaba da gudana yayin da hukumomin tsaro ke kara zage damtse domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin Jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Borno: Boko Haram ta saki bidiyon tsohon Mataimakin Ciyaman da ta sace

An kai wa Hausawa hari a Kudancin Najeriya

A baya, mun wallafa cewa fusatattun matasa sun kai hari kasuwar sayar da dabbobi da ke Ekpoma a Edo ta Tsakiya, inda suka kori ’yan kasuwar Hausawa tare da yanka dabbobinsu.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya biyo bayan wata zanga-zanga da mazauna yankin suka yi, bayan gano gawar wani matashi da ake zargin masu garkuwa da mutane sun kashe shi a yankin.

Wannan lamari ne da ya kara tayar da hankalin jama’a, lamarin da ya rikide zuwa tashin hankali a kasuwar dabbobi, inda matasan suka mamaye kasuwar, suna korar Hausawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng