'Yan Sanda Sun Fasa Kofa, An Ga Gawarwarin Mutum 6 da Suka Kwanta Barci

'Yan Sanda Sun Fasa Kofa, An Ga Gawarwarin Mutum 6 da Suka Kwanta Barci

  • 'Yan sanda sun fasa kofar gida, sun ciro gawarwakin mutane shida 'yan gida daya da suka mutu bayan sun kwanta barci a Ribas
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa hayakin janareta ne ya yi ajalin mutanen
  • Kwamishinan 'yan sandan Ribas ya ja hankalin mutane su guji kunna janareta a wuraren da suke kwanciya barci don kauce wa matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - An gano gawarwakin mutane shida 'yan gida daya a gidansu da ke kauyen Ogale Eleme, a Karamar Hukumar Eleme ta Jihar Rivers.

An ruwaito cewa an gano gawarwakin ne a ranar Lahadi, bayan jami’an ‘yan sanda sun fasa kofar gidan da misalin karfe 3:00 na rana.

Jihar Ribas.
Taswirar jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar ‘yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a Fatakwal, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Halin da masu zuwa Mauludi suke ciki bayan kwashe kwanaki hannun 'yan bindiga a Plateau

An gano abin da ya kashe iyalai a Ribas

Kakakin 'yan sandan ta ce binciken farko ya nuna cewa hayakin janareta na iya zama sanadin mutuwar iyalan.

Ta ce ana zargin sun yi kuskuren barin janareta a kunne yana aiki a falo, yayin da duka mutanen gidan suka kwanta barci.

A cewarta, an fara cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa mutuwar mutanen idan har labarin da Vanguard ta ruwaito ya tabbata.

“Rundunar ‘yan sandan Ribas na bakin cikin sanar da wani mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Janairu, 2026, a Ogale Eleme, inda aka gano mutum shida yan gida daya duk sun mutu a cikin daki a kulle,” in ji ta.

Yadda labari ya kai wurin 'yan sanda

Iringe-Koko ta bayyana cewa wani 'dan uwan mamatan ne ya sanar da ‘yan sanda faruwar lamarin.

“Wani mutumi, Godwin Ogosu, da ke Ogale Eleme ne ya kai rahoton gaggawa cewa yayansa, matarsa da ‘ya’yansa da suka kwanta barci tun daren jiya ba su farka ba, duka kofofin gidan a kulle,” in ji ta.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari 'wurin shakatawa' na gwamnatin tarayya

Wane mataki 'yan sanda suka dauka?

Ta kara da cewa jami’an ‘yan sanda daga ofishin Eleme sun kai dauki cikin gaggawa, kuma daga isa wurin suka fasa kofar, suka tarar mutanen gidan duk sun mutu.

Iringe-Koko ta kara da cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda, Olugbenga Adepoju, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Jami'an yan sanda.
Dakarun rundunar 'yan sandan Najeriya suna fareti Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter
“Kwamishinan ‘Yan Sanda ya shawarci jama’a da su rika ajiye janareta a wuri mai iska, nesa da kofofi, tagogi da mashigar iska, ba a cikin falo, gareji ko daki ba domin kauce wa gubar gubatacciyar iskar ,” in ji ta.

Mutum 8 'yan gida daya sun mutu

A wani labarin, kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Imo ta tabbatar da mutuwar wasu yan gida daya su takwas a wani mummunan hatsarin mota.

Lamarin wanda ya afku da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Juma'a, ya jefa al'ummar yankin cikin bakin ciki.

A cewar wanda abun ya faru kan idonsa, jami'an yan sanda da al'ummar yankin sun fasa motar cikin hawaye domin fitar da gawarwakin iyalin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262