'Yan Bindiga Sun Farmaki Amarya da Wasu 'Yan Gidan Biki, An Rasa Rayukan Bayin Allah
- 'Yan bindiga sun farmaki 'yan gidan biki a yankin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, sun kashe mutane biyu
- Bayanai sun nuna cewa maharan sun kuma raunata wasu da dama ciki har da amarya, sun kuma yi awon gaba da mutane da yawa
- Wannan na zuwa ne a lokacin da gwamnatin Katsina ke kokarin sakin mutum 70 da ake tuhuma da hannu a ayyukan ta'addaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Wasu mahara da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kan tawagar biki a Unguwar Nagunda, Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina.
Bayanai sun nuna cewa yan bindigar sun kashe akalla mutane biyu daga tawagar masu zuwa biki a harin yayin da wasu da dama, ciki har da amarya, suka jikkata.

Source: Original
'Yan bindiga sun farmaki 'yan biki a Katsina
Tashar Channels tv ta ce a yayin harin da ya faru a daren Lahadi, yan bindigan sun yi awon gaba da bakin da suka halarci biki da dama, kuma har yanzu ba a san adadinsu ba.
Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa mazauna yankin sun ji karar harbe-harbe, lamarin da ya jefa su cikin fargaba sosai bayan ‘yan bindigar sun shiga kauyen a daren Lahadi.
“Har zuwa safiyar yau, mutanen gari na ci gaba da tantancewa domin sanin adadin mutanen da aka sace,” in ji majiyar.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq, domin yin karin bayani, bai amsa kiran waya ko sakonnin tes ba har zuwa lokacin da hada wannan rahoto.
Gwamnatin Katsina za ta saki 'yan bindiga
Harin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Katsina ke shirin sakin mutane 70 da ake zargi da hannu a ayyykan ta’addanci

Kara karanta wannan
Babbar magana: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari 'wurin shakatawa' na gwamnatin tarayya
Gwamnatin ta ce za ta saki mutanen ne a wani bangare na karfafa yarjejeniyar zaman lafiya da ake ganin ta samu tsakanin yankunan da ke fama da matsalar tsaro da kuma ‘yan bindiga.
Ta kuma bayyana cewa yarjejeniyar zaman lafiya ta taimaka wajen sakin akalla mutane 1,000 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a hare-hare daban-daban a jihar Katsina.

Source: Facebook
A ranar 2 ga Janairu, 2026, aka ga wata takarda da ke nuna shirin gwamnatin jihar Katsina na sakin ‘yan bindigar da ake tsare da su wadanda ke fuskantar shari’o’in laifuka.
A cikin takardar, gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Radda ta nemi taimakon Kwamitin Kula da Aiwatar da Shari’a (ACJMC) domin sakin wadanda ake tsare da su cikin sauki
'Yan bindiga sun farmaki kauyuka a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Shaidun gani da iso sun bayyana cewa hare-haren sun faru ne a daren Litinin, 5 ga watan Janairun 2025 lokacin da ’yan bindigar suka shiga yankin.
Majiyoyin tsaro sun ce ’yan ta’addan sun fara kai hari ne a Unguwar Alhaji Barau, daga nan suka wuce zuwa Gidan Dan Mai-gizo da kuma Gidan Hazo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
