"Ina Ya Shiga?" Peter Obi Ya Fito da Damuwarsa game da Yawan Tafiye Tafiyen Tinubu
- Peter Obi ya soki tafiye-tafiyen da Shugaba Bola Tinubu ke yi zuwa kasashen waje inda ya ce ya kwashe kwanaki akalla 196 a waje
- 'Dan takarar shugaban kasa a 2023 ya nuna takaicinsa kan yadda Tinubu ke yawo a kasashen waje alhalin Najeriya na cikin "wani hali"
- Ya ce rashin jawabin sabuwar shekara da shiru kan matsalolin tsaro na nuna rashin kishin talakawa da gazawar gwamnatin Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya nuna damuwarsa kan abin da ya kira rashin jagoranci a Najeriya.
Peter Obi ya jefo tambaya game da inda Shugaba Bola Tinubu ya shiga a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Source: UGC
"Ina shugaban Najeriya ya shiga?" - Peter Obi

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Masana sun hango babban kalubale da Tinubu zai iya fuskanta a 2026
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, 12 ga Janairu, 2026, Obi ya bayyana cewa Najeriya tana cikin wani hali, amma shugaban ƙasar ya kwashe kusan rabin lokacinsa a ƙasashen waje maimakon ya tunkari matsalolin da ke damun talakawa.
Peter Obi ya yi wannan tambayar ne a matsayin neman bahasi daga shugaban ƙasa, inda ya bayyana cewa kusan ’yan Najeriya miliyan 140 ne ke rayuwa cikin matsanancin talauci.
Ya ƙara da cewa matsalolin yunwa, rashin tsaro, da rashin aikin yi ga matasa miliyan 80 sun jefa ƙasar cikin rudani.
“A tsakiyar wannan rudani, ina shugabanmu yake? Ya kwashe kwanaki 196 a ƙasashen waje a shekarar 2025 kaɗai—fiye da lokacin da ya kwashe a cikin ƙasarsa, a lokacin da muke fuskantar manyan rikice-rikice,” in ji tsohon gwamnan na Jihar Anambra.
Obi ya kuma soki shugaban kan rashin yi wa ’yan ƙasa jawabi a farkon sabuwar shekarar 2026, sannan ya bayyana damuwa kan yadda shugaban ya yi shiru bayan harin sama da Amurka ta kai a yankin Sokoto.
Bola Tinubu ya dura Abu Dhabi
A yayin da Peter Obi ke neman shugaban kasar, rahoton jaridar Legit Hausa ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya bar Legas ne ranar 28 ga Disamba don hutu a Turai.

Kara karanta wannan
Wike ya maida martani ga masu bukatar Tinubu ya tsige shi daga kujerar Ministan Abuja
Sannan a ranar Lahadi ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) domin halartar taron mako na dorewar muhalli na shekarar 2026, bisa gayyatar Shugaba Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X cewa:
"Shugaba Tinubu ya isa Abu Dhabi ne bayan ya baro Turai, inda ya gudanar da wani bangare na hutunsa na karshen shekara, kuma har ya tattauna da shugaban Rwanda, Paul Kagame da shugaban Faransa, Emmanuel Macron.
"Wannan ziyara ta Tinubu zuwa Abu Dhabi ta sake karfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da kasashen Larabawa, yayin da Najeriya ke sahun gaba a tattaunawar dorewar muhalli."

Source: Twitter
Peter Obi ya dage kan kuskuren Tinubu
Peter Obi dai ya jaddada cewa ba za a iya gudanar da mulkin Najeriya kamar kasuwancin kashin kai ko ƙungiyar sirri ba.
Ya ce shugabanci na gari yana buƙatar tattaunawa kai-tsaye da jama'a da kuma kasancewa tare da su a lokacin da suke cikin damuwa.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ƙare da cewa, shiru a lokacin da ƙasa ke cikin rikici ba komai ba ne face 'nuna babbar gazawa'.
Kudu sun goyi bayan tazarcen Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugabannin APC na Kudu maso Gabas sun ayyana goyon baya ga Bola Tinubu a zaben 2027 domin tabbatar da cigaba da samun daidaito.
Wannan mataki ya zo ne kwanaki kadan bayan Peter Obi ya ayyana niyyar tsayawa takara a jam'iyyar ADC domin kalubalantar jam'iyya mai mulki idan har ya dace da tikiti.
Gwamnonin Kudu maso Gabas sun aika sako ga 'yan takarar shugaban kasa cewa ba za su sake yarda a rarraba kuri'un Inyamurai ba don kare muradin yankinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
