Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 40 a Zamanantar da Gadar Legas da CCTV

Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 40 a Zamanantar da Gadar Legas da CCTV

  • Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabuwar cibiyar kula da kyamarorin CCTV domin sa ido a gadar Third Mainland da ke Legas, a wani mataki na ƙarfafa tsaro
  • Ministan ayyuka na kasa, David Umahi, ya ce aikin ya biyo bayan manyan gyare-gyare da aka yi wa gadar tun bayan hawar wannan gwamnati a 2023
  • Cibiyar za ta bai wa jami’an tsaro damar sa ido kai-tsaye, hana gudun da ya wuce kima, da kuma ɗaukar matakin gaggawa idan wani abu ya faru a wajen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wata sabuwar cibiyar kyamarorin CCTV da aka kashe Naira biliyan 40 wajen gina ta, domin sa ido kan gadar Third Mainland, daya daga cikin manyan gadoji mafi muhimmanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana maganar shiga APC, Abba Kabir ya caccaki Ganduje, ya yabi Kwankwaso

An kaddamar da cibiyar ne a wani bikin da Ministan Ayyuka, David Umahi, ya jagoranta, inda ya bayyana cewa aikin na cikin kokarin gwamnati na inganta tsaro da lafiyar masu amfani da gadar.

Hotunan yadda CCTV ke aiki a gadar Legas
Yadda aka kaddamar da CCTV a gadar Legas. Hoto: Lagos State Megal City
Source: Facebook

Rahoton Channels TV ya nuna cewa gwamnatin ta ce cibiyar za ta taimaka wajen hana tuki mai hatsari, dakile yunkurin kashe kai, da sauransu.

Dalilin kafa cibiyar CCTV a Legas

Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa lokacin da gwamnatin Tinubu ta hau mulki a shekarar 2023, ta tarar da gadar Third Mainland cikin mummunan yanayi.

Vanguard ta rahoto ya ce gadar, tare da gadar Carter da ta Iddo, sun bukaci gyara a sama da kuma karkashin ruwa bayan cikakken bincike da aka yi.

Umahi ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da aikin gyaran gadar, ciki har da sauya manyan kayan fadada gadar, domin inganta ta da kuma saukaka zirga-zirga.

Yadda tsarin CCTV zai yi aiki a gadar

A bayanin da ya yi, ministan ayyuka ya ce an tsara CCTV tun 2025 a gadar domin ganin duk abin da ke faruwa a kanta a kowane lokaci.

Kara karanta wannan

Sanatan Najeriya ya gina danƙareren gida, talakawa sun masa rubdugu a intanet

Jami’an tsaro za su kasance suna kallon hotuna kai-tsaye daga cibiyar, tare da daukar mataki kan masu karya dokokin hanya, musamman gudun da ya wuce kima.

Ya kara da cewa an tanadi jirgin ruwa na sa ido da kuma motocin Hilux guda biyu, wadanda za a mika wa rundunar ’yan sanda domin taimakawa sa ido da daukar matakin gaggawa idan wani lamari ya taso.

Ministan ayyuka na Najeriya
Ministan ayyuka na kasa, Dave Umahi. Hoto: @FMWNIG
Source: Twitter

Umahi ya yi kira ga direbobi da su mutunta dokokin hanya, yana mai cewa yawan gudu na daga cikin manyan dalilan hatsari a gadar.

Bayanin jami'in gwamnatin Legas

Mai kula da ayyukan gwamnati a Legas, Olufemi Dare, ya bayyana cewa wannan cibiyar ita ce irinta ta farko a kan kowace gada a Najeriya.

A cewarsa, aikin ya kunshi na’urorin sola guda 240, injinan wutar lantarki 10, na’urar wuta mai karfin 300 kVA, janareta, manyan allunan kallo da sauransu.

Har ila yau, aikin ya hada da fitilun titi masu amfani da hasken rana guda 1,268 da kuma rijiyar ruwa, inda Dare ya ce an riga an biya kusan Naira biliyan 36 daga cikin Naira biliyan 40.17 na kwangilar.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara

Za a kafa cibiyar kayan gini a Legas

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta amince da filin da aka ware a jihar Legas domin kafa cibiyar kayan gine-gine.

Rahotanni sun bayyana cewa za a kafa cibiyar a Legas a karon farko kafin daga bisani a wace sauran yankunan Najeriya.

Ministan gidaje da raya birane ya bayyana cewa Kano da Gombe na cikin jihohin da za su biyo baya bayan gama wa da Legas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng