CCTV ya naɗi wata mata tana barbaɗa 'garin magani' a harabar kotu kafin a yanke mata hukunci

CCTV ya naɗi wata mata tana barbaɗa 'garin magani' a harabar kotu kafin a yanke mata hukunci

  • A wani bidiyo wanda kamarar CCTV ta dauka ranar Laraba 22 ga watan Satumba da misalin karfe 7:45 na safe an ga wani lamari mai ban tsoro
  • A bidiyon an ga wata mata ta zage tana barbada wani gari da ake zargin na tsafi ne a bakin kofar wata kotun majistare wanda ta ciro daga jakarta
  • Daga baya an gano cewa bincike ake yi akan ta kafin alkalin kotun ya yanke mata hukuncin da ya dace da laifin da ake zargin ta aikata

Kenya - A ranar Laraba, 22 ga watan Satumba 2021 kamarar CCTV ta dauki bidiyon wata mata mai matsakaicin shekaru tana barbada wani gari da ake zargin na tsafi ne a bakin kofar kotun majistare ta Shanzu a kasar Kenya.

An samu labari akan yadda aka kai korafin Veronica Ndinda Mutisya kotun majistaren, sai ga shi kuma an kama ta tana barbada wani garin magani wanda ake zargin na tsafi ne bayan ta fito da shi daga jakar ta.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bincike ya nuna abinda ya kashe budurwar da aka tsinci gawarta cikin motar basarake da ya tsere

CCTV ya naɗi wata mata tana barbaɗa 'gishiri' a harabar kotu kafin a yanke mata hukunci
Kotun Majistare a Kasar Kenya. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Tuni ‘yan sanda suka nufi ofishin su don ta amsa tambayoyi

Yanzu haka ‘yan sanda sun tafi da ita ofishin su na Bamburi don su ci gaba da bincike akan ta bayan bayyanar bidiyon.

Daga bidiyon CCTV din, an ga Mutisya ta isa harabar kotun da misalin karfe 7:45. Tana zuwa bakin kofar kotun sai ta ciro wani farin gari daga jakar ta. Daga nan ne aka gan ta tana barbada garin a kofar kafin daya daga cikin masu share harabar ya kama ta.

An fara jefa mata tambayoyi har da kiran mai kula da kotun sannan ‘yan sanda suka zo suka tafi da ita.

A cewar ta gishiri ne take barbadawa ba wani abu ba

Yayin kare kan ta, Mutsiya ta ce garin gishiri ne da wani gari na daban da dama take ajiyewa a jakar ta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yan fasa kwabri da mota makare da soyayyun kaji

Kamar yadda ta ce:

“Ina amfani da shi ne idan rai na a bace yake. Ba wai don inyi tsafi don canja sakamakon hukuncin da za a yanke min ba. Ina neman famfo ne don in wanke hannaye na a harabar kotun.”

Yanzu haka ana ci gaba da bincike akan lamarin.

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Kara karanta wannan

Ethiopia: Abubuwa 5 game da kasar da ta fara karbar Musulunci, ba a yi mata mulkin mallaka ba

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel