Ministan Tsaro Ya Yi Bayani game da Sabon Shirin Tinubu kan Matsalar Tsaro

Ministan Tsaro Ya Yi Bayani game da Sabon Shirin Tinubu kan Matsalar Tsaro

  • Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu na sane matsalolin tsaron Najeriya
  • Ministan ya bayyana cewa yanzu haka, Shugaba Tinubu ya bayar da umarni na ƙarfafa gwiwar sojoji da hukumomin tsaro da kayan aiki
  • Majalisar Dokoki ta tabbatar da haɗin kai da zartarwa domin dawo da zaman lafiya a duka sassan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana da umarni wajen tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro suna da isassun kayan aiki.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce Tinubu ya kara da bayar da umarni a ba ma'aikatan tsaron kuluwa ta musamman, tare da ƙarfafa musu gwiwa domin karkade miyagu daga sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: An jibge jami'an tsaro, motocin yaki a kofar gidan gwamnatin Kano

Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce Tinubu ya zage damtse kan tsaro
Janar Christopher Musa mai ritaya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: HQ Nigerian Army/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin taron addu’ar haɗin kan mabiya addinai na Kirista domin bikin ranar tunawa da girmama sojoji (AFCRD) ta shekarar 2026 a Abuja.

Taron ya samu halartar Shugaban Rundunar Tsaro ta Ƙasa (CDS), Janar Olufemi Oluyede, Sufeto Janar na ’Yan Sanda (IGP) Kayode Egbetokun, tare da matansu.

Bola Tinubu ya samu yabo kan tsaro

Arise News ta wallafa cewa Ministan ya gode wa Shugaba Tinubu bisa cikakken goyon baya da jajircewarsa wajen kula da jin daɗin sojoji da iyalansu.

Ya ce ayyukan Shugaban ƙasa suna nuna girman darajar da yake bai wa hidima da sadaukarwar da dakarun ke yi wajen ceto Najeriya.

A kalalamsa:

“Mun yi addu’a Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da ba shi hikima, ƙarfi da shiriya yayin da yake jagorantar ƙasarmu."

Ya kuma bayyana cewa duk da ƙalubalen tsaro da tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta, yana da kyakkyawan fata cewa Najeriya za ta shawo kansu.

Kara karanta wannan

Fubara: Majalisar dokokin Ribas ta ja kunnen masu yunkurin hana ta tsige Gwamna

Ministan tsaro ya jinjinawa sojoji

Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya ya gode wa dakarun sojoji da jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen kare ƙasa.

Ya ce:

“Wannan rana ta ibada ce, ta tunani da tunawa. Mun taru a nan da kuma a coci-coci a jihohi 36, muna dogaro da alkawarin Ubangiji kamar yadda aka rubuta a Irmiya 29:11."
Christopher Musa ya ce Tinubu na girmama sojoji
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin bikin tunawa da sojojin kasar Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Ministan ya jaddada cewa ana girmama jaruman maza da mata da suka ba da rayukansu wajen kare ƙasa, yana mai cewa sadaukarwarsu ba za ta taɓa gushewa daga tarihin Najeriya ba.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Majalisar Dokoki tare da bangaren zartarwa sun kuduri aniyar dawo da Najeriya cikin ƙasashen Afrika mafi zaman lafiya da tsaro.

Tinubu ya kafa sabon tsarin tsaro

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sunayen wasu kungiyoyi shida da gwamnatinsa za ta rika ɗauka a matsayin ‘yan ta’adda, bisa sabon tsarin tsaro da yake shirin aiwatarwa.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun kara kaimi a yaki da 'yan bindiga a jihohin Arewa 2

Shugaban ya ce wannan mataki na daga cikin manyan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke kawowa domin dakile matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan, musamman sassan Arewacin Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar dokoki ta 'kasa, inda ya jaddada kudirin tabbatar da tsaro a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng