Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kashe Sojan Najeriya da Wani Jami'in NSCDC

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kashe Sojan Najeriya da Wani Jami'in NSCDC

  • Wasu yan bindiga sun kashe soja guda daya da jami'in Civil Defence a jihar Benue yayin da suke kan hanyar dawowa daga kasuwa
  • Harin ya tilasta wa daruruwan mazauna garin Udeku tserewa daga gidajensu yayin da harkokin yau da kullum suka tsaya cik a yankin
  • Jami'an tsaron da aka kashe na daga cikin dakarun da aka tura domin dakile hare-haren makiyaya dake addabar yankunan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Wasu da ake zargin makiyaya ne ɗauke da makamai sun kashe wani soja da kuma jami'in hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a Benue.

'Yan bindigan sun aikata wannan danyen aikin ne a garin Udeku da ke gundumar Turan, ƙaramar hukumar Kwande a Jihar Benue.

'Yan bindiga sun hallaka soja da jami'in NSCDC a Benue
Dakarun sojojin Najeriya suna tafiya a hanyar zuwa wani kauye, a wani aikin tabbatar da tsaro. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Benue: An kashe soja da jami'in NSCDC

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Kotu ta ba da umarnin wucin gadi a shari'ar gwamnati da likitoci

Lamarin, wanda ya faru a ranar Asabar 10 ga Janairu, 2025, ya jefa mazauna yankin cikin fargaba, inda mutane da dama suka tsere daga gidajensu, yayin da harkokin yau da kullum suka tsaya cik, in ji rahoton Punch.

Wani jagoran al'umma a yankin, Mista Lawrence Akerigba, ya tabbatar da cewa jami'an tsaron da aka kashe suna cikin rukunin dakarun da aka tura yankin ne domin wanzar da zaman lafiya sakamakon yawan hare-haren da ake kai wa manoma.

NSCDC ta bayyana cewa jami'inta da aka kashe, CCA Tijani Idris (mai lambar aiki 76691) ya fito daga rundunar ta jihar Kaduna, wanda aka tura aikin haɗin gwiwa Benue karkashin Operation Whirl Stroke.

Yadda aka yi wa jami'an tsaro kwanton bauna

Rahotan jaridar Tribune ya nuna cewa jami'an tsaron biyu suna kan hanyarsu ta dawowa ne daga kasuwar Aga a kan babur, inda suka je sayo gas din girki.

Sai dai kwatsam, suka faɗa wani tarko da 'yan ta'addar suka dana a kan hanya, kamar yadda suka saba yi idan za su kai wa mutane hari.

“Sun yi musu kwanton ɓauna ne, inda suka buɗe musu wuta nan take suka kashe su,” in ji wata majiya.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An tabbatar da mutuwar kasurgumin 'dan bindiga a Najeriya

Matasan yankin sun haɗa kai inda suka shiga daji suka kwaso gawarwakin jami'an, waɗanda aka kai su ɗakin ajiye gawa da ke Jato Aka.

Yankunan jihar Benue na kasa fuskantar hare-haren 'yan bindiga
Taswirar jihar Benue, inda ake zargin 'yan bindiga sun kashe soja da jami'in NSCDC. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hare-haren 'yan bindiga sun karu a Benue

Wannan hari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da maharan suka kashe manoma biyar a yankin makon da ya gabata.

Masana na nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar hare-hare kan jami'an tsaro da manoma a Benue tun bayan harin sama da Amurka ta kai kan sansanonin ISWAP a Sokoto ranar 25 ga Disamba, 2025.

Rundunar NSCDC ta jaddada cewa duk da wannan rashi, za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙar rashin tsaro a kowane fanni.

'Yan bindiga sun farmaki Benue Link

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun harbi fasinjoji uku dake tafiya a cikin motar kamfanin Benue Links kusa da garin Otukpo a daren Asabar.

Babban manajan kamfanin sufurin ya tabbatar da cewa fasinjojin suna karbar magani sannan kamfanin zai biya dukkan kudaden asibitin.

Hukumar sufurin ta sake jaddada dokar hana tafiyar dare ga dukkan direbobinta domin kaucewa fadawa tarkon yan bindiga a hanyoyin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com